An zargi Gwamnan jihar Ribas da nuna wariya ga cigaban kasuwancin ƴan Arewa

Daga Habu Ɗan Sarki

Ƙungiyar haɗin kan marubuta a kafafen sada zumunta na Soshiyal Midiya, ta Arewa Media Writers ta bayyana damuwa game da ƙalubalen da Hausawa mazauna Jihar Ribas ke fuskanta na rusa harkokin su na kasuwanci, ƙuntatawa rayuwar su da suke zargin Gwamnan jihar Nyeson Wike da sa hannun a ciki.
A cikin saƙon da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Kwamred Abba Sani Pantami ya sanya wa hannu, ƙungiyar ta koka da irin ƙuntatawar da ta ce Gwamnan Jihar na yi wa ýan Arewa mazauna jihar, musamman biyo bayan rushe kasuwar da ýan Arewan suke harkokin su fiye da shekaru 40 da suka gabata, duk kuwa da yadda suke kiyaye dokokin jihar da biyan haƙƙokin da ake sanya musu.

An zargi Gwamnan jihar Ribas da nuna wariya ga cigaban kasuwancin ƴan Arewa
Gwamnatin jihar Kebbi ta ƙaddamar da motocin yaƙi da ta ƙera wa sojoji

Shugaban ƙungiyar Arewa Media Writers na Jihar Ribas, Malam Murtala Adam ya shaidar da cewa, tun daga watan Maris na shekarar da ta gabata lokacin da aka rufe kasuwanni sanadiyyar cutar annobar COVID-19, Gwamnan ya sa aka gana harkoki a kasuwar, duk kuwa da kasancewar sauran kasuwannin jihar an sake buɗe su daga baya.
Zargin da ýan Arewa mazauna birnin Fatakwal ke yi shi ne na Gwamnan Jihar na nuna musu wariya da tauye hakki a matsayin su na ýan Nijeriya, duk kuwa da kasancewar kasuwar da suke harkokin su a ciki mallakin Gwamnatin Tarayya ce.
A dalilin rusa wannan kasuwa dai yanzu haka a cewar ƙungiyar ƙarƙashin jagorancin Kwamred Abba Sani Pantami, mutane da dama sun shiga wani mummunan hali, wasu sun gamu da lalurar hawan jini da shanyewar wasu gaɓoɓin jiki, wasu ma har sun rasu, saboda ƙunci da baƙin cikin lalata musu dukiya da gwamnatin jihar ta sa aka yi.
Ƙungiyar ta nemi Gwamnatin Tarayya, Majalisar Gwamnonin Arewa, ministoci ýan Arewa, sanatoci da ke wakiltar yankin Arewa, ýan majalisun jihohin Arewa da sauran masu faɗa a ji na yankin Arewa da su kai wa al’ummar Arewa da ke zaune a yankin ɗaukin gaggawa.

Tura Wa Abokai

An wallafa wannan Labari September 22, 2021 9:47 PM