Kotu ta daure matasan da suka watsa bidiyon batsa tsawon shekaru 4 a Sokoto

Kotun majistare dake jihar Sokoto ta yanke wa wasu matasa uku hukuncin zaman kurkuku na tsawon shekara 4 da rabi dalilin kamasu da laifin watsa bidiyon tsiraici da abokin su ya dauka na bayan yayi lalata da wata yarinya sannan suka saka a yanar gizo.

Kotun ta yanke wa Aminu Hayatu-Tafida, Umar Abubakar da Mas’ud Gidado wannan hukinci ranar Talata.

Dan sandan da ya shigar da karar ASP Samuel Sule ya ce rundunar ta kama wadannan mutane a ranar biyar ga Oktoba 2020.

Sule ya ce rundunar ta kama mutanen ne bayan mahaifin yarinyar da aka dauki bidiyonta na batsa dake zama a Bardon Barade ya shigar da kara a ofishinsu.

Ya ce wata rana a shekarar 2017 Hayatu-Tafida ya dauki yar sa lokacin shekaranta 16 ya kai ta Otel din ‘Phoenix Guest Inn’ inda ya yi lalata da ita sannan ya dauki bidiyonta tsirara na tsawon sakan 18.

Bayan Hayatu-Tafida ya nuna wa abokansa biyu bidiyon sai suka saka bidiyon a yanar gizo.

Sule ya ce hakan da suka yi ya sa an dakatar da auren yarinyar da za a yi a Oktoba 2020.

Alkalin kotun Shu’aibu Ahmad ya amince da rokon sassauci da matasan suka yi saboda wannan shine karon farko da suke aikata laifi irin haka.

Ahmad ya yanke wa musa hukuncin zama a kurkuku na tsawon shekara biyu ko su biya taran Naira 200,000 bisa laifin daure wa abokinsugindi da suka yi.

Sannan bisa ga laifin mara wa juna baya za su yi watanni 6 a kurkuku ko kowanen su ya biya belin Naira 50,000.

Ahmad ya ce kowanen su zai biya mahaifin da yarinyar naira 100,000.