AN YANKA TA TASHI: Buhari na so ya yi wa Sabuwar Dokar Fetur Kwaskwarima

Shugaba Muhammadu Buhari ya nemi Majalisar Dattawa ta amince masa ya yi wa wasu ‘yan gyare-gyare a Sabuwar Dokar Fetur ɗin da ya sa wa hannu cikin watan jiya.

A cikin wasiƙar da ya aika wa Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmed Lawan, Buhari ya ce ya na son yin kwaskwarimar ce a ɓangaren gudanarwar tsare-tsaren Hukumoni Biyu, wato ‘Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority’ da kuma Nigerian Upstream Regulatory Commission.’

Sannan kuma Shugaba Buhari ya gabatar da sunayen mambobin hukumar gudanarwar waɗannan hukumomin biyu. Kuma ya aika sunayen na su a lokaci guda tare da wasiƙar neman amincewar ya yi wa PIA kwaskwarima.

Wasiƙar dai Shugaban Majalisar Dattawa da Shugaban Majalisar Tarayya duk sun karanta su a Zauren Majalisa kafin a fara zaman ranar Talata.

Buhari ya ce naɗa wa hukumar ɗaya shugaban hukumar gudanarwa da sauran mambobi na cikin Dokar Fetur ta 34(3) ta 2021.

Waɗanda Buhari ya miƙa sunayen na su sun haɗa da:

Idaere Ogan, Shugaba, Sarki Auwalu Babban Darakta, Abiodun Adeniyi Babban Daraktan Kuɗi da kuma Ogbugo Ukoha, Daraktan Ajiya da Rarraba Mai.

Hukumar ta biyu kuma an naɗa mata Isa Ibrahim Modibbo, Gbenga Komolafe, Hassan Gambo, Rose Ndong.

Buhari ya nemi Majalisa ta amince a yi gyaran da za a riƙa naɗa wa hukumomin mambobi shida kowace, domin kowane domin a kowane yankin ƙasar nan ya samu wakilci a ciki.

Idan ba a manta ba, an kai ruwa rana sosai kafin Shugaba Muhammadu Buhari ya sa wa Sabuwar Dokar Fetur Hannu, bayan da ƙudirin ya shafe shekaru 12 a Majalisa ana ce-ce-ku-ce a kan sa.