EFCC ta damƙe bokayen da su ka ci Naira miliyan 16 don azurta mai son banza cikin gaggawa

Jami’an Hukumar EFCC ta damƙe wani boka da ɗan-koren sa a Jihar Barno, bayan sun zambaci wani mai son banza har naira miliyan 16.

Bokan mai suna Mohammed Ibrahim, an kama shi tare da ɗan-koren sa mai suna Ibrahim Abubakar, bayan sun damfari wani mai suna Mohammed Gaji.

Haka dai sanarwar da Kakakin Yaɗa Labarai na EFCC, Wilson Uwujaren ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.

Cikin sanarwar, Uwujaren ya ce mutanen biyu sun damfari Gaji Naira miliyan 16 bisa sharaɗin za su yi masa tsatsube-tsatsube, surkulle da kuma addu’o’in da zai kuɗance lokaci ɗaya.

EFCC ta ce an bankaɗo wannan harƙalla ce bayan da wani ya kai wa hukumar ƙorafin cewa ya bai wa Gaji kuɗi har Naira miliyan 22 domin su yi jarin sana’ar kiwon shanu.

“Maimakon Gaji ya je ya haɗa garken shanun Naira miliyan 22, sai ya bai wa Mohammed Ibrahim da ɗan-koren sa Naira miliyan 16, domin su yi masa addu’ar yadda zai kuɗance kafin ƙiftawar ido.”

An cafke su Sabon Bolori, bayan Chadi Bashin a Jihar Barno.

Za a maka su ukun kotu da zarar an kammala bincike.

Wani mai suna Mohammed Alhaji Bukar ne ya kai rubutaccen ƙorafi kan Gaji a ofishin EFCC, bayan ya ba shi Naira miliyan 22.2 domin yin sana’ar kiwon shanu, amma kuɗaɗen su ka salwanta.

Yayin da jami’an EFCC su ka kai farmakin cafke shi, an samu wani wani wawakeken rami a cikin ɗakin sa, wanda aka lulluɓe da fatar dabba da teburi.

A cikin ramin ne aka ce ɗan-koren bokan ke shigewa ya na maƙe murya, ya na kwaikwayon maganar aljanu.

Gaji ya ce bokayen sun ba shi wani dutse mai tsada, wani akwatin ƙarfe mai ɗauke da farin ƙyalle da kuma wasu kuɗaɗen ƙasashen waje.

Ya ce sun umarce shi ya yi azumin wata uku da kwana ɗaya. Kuma ya na kammalawa zai kuɗance.

Tarkace da tambotsan da EFCC su ka kwaso a ɗakin bokayen sun haɗa da fararen tufafi, ƙorai, fatun dabbobi, ƙahon wata dabba, kuɗaɗen waje da kuma ƙananan akwatin ƙarfe.