AN YANKA TA TASHI: Ƙungiyar Malaman Jami’o’i sun ce digirin-digirgir ɗin Pantami na ‘Jam’ar ‘Jatau Na Albarkawa ne’

Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa (ASUU) sun yanke hukunci tare da ɗaukar matsayin cewa Digirin-digirgir na Farfesan da aka ba Ministan Sadarwar, Isa Pantami, haramtacce ne, don haka ba su yarda da shi ba.

Sun bayyana hakan ne bayan tashi daga taron su na tsawon kwanaki biyu da suka gudanar a Jami’ar Legas.

Majalisar Zartaswar ASUU ta ce ta bi diddigin yadda Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Owerri (FUTO) ta bayar da muƙamin Farfesan Nazarin Kare Aikata Laifuka a Kafafen Sadarwar Zamani (Cyber security) cewa an kauce wa ƙa’ida da matakan da suka kamata ya bi kafin ya kai ga matsayin.

Shugaban Ƙungiyar Malaman Jami’o’i ta Ƙasa, Emmanuel Osodeke, ya ce: “Majalisar Zartaswar ASUU ta yi Allah-wadai da matsayin ‘Farfesan’ da aka bai wa Dr. Isah Ali Ibrahim Pantami.

“Daga hujjojin da muka tattara kuma muka tabbatar, Dakta Pantami bai cancanci muƙamin Farfesa ba. Sannan kuma ba shi matsayin ya kauce wa tsari, matakai da ƙa’idojin da ya kamata ya bi kafin ya zama farfesa. Kuma kowa ko a wace jami’a ce, sai ya bi waɗannan hanyoyi da matakai sannan ya ke zama farfesa a jami’a.

“Majalisar Zartaswar ASUU na kira ga dukkan mambobin ta da sauran rassan ƙungiyar na faɗin ƙasar nan, kada su amince kuma kada su riƙa bai wa Pantami girman da ake bai wa Farfesa.”

ASUU ta ce matsayin da ta ɗauka a yanzu ƙarin jaddadawa ce kan matsayin ta na farko da ta ɗauka cikin 2021.

Daga nan ta ce dukkan mambobin ta da su ke da hannu wajen cuku-cukun bai wa Pantami matsayin farfesa, za a hukunta su, don na baya su ɗauki darasi.