An sace miliyan N345m na magada a asusun kotun Shari’ar musulunci a Kano

Naira miliyan 345 ya yi batan dabo daga asusun Babbar Kotun Shariah Musulunci ta jihar Kano, a cewar wani rahoto da Freedom Radio ta fitar.

Babban Khadi na jihar Kano Tijjani Yakasai ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an kai rahoton lamarin ga Hukumar Karbar Ƙorafe-ƙorafe da Yaƙi da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, PCACC, don gudanar da bincike.

  • An sace miliyan N345m na magada a asusun kotun Shari’ar musulunci a Kano
  • Rundinar soji za ta koma amfani da tauraron ɗan’adam wajen sadarwa

Sakataren kotun, Haruna Khalil ya ce an kafa kwamitin bincike da zai binciki lamarin.

A cewarsa, kuɗaɗen na magada ne kuma magadan ne suka ajiye su a asusun kotu kafin a raba su ga waɗanda ke da haƙƙi.

Ya ce an gano bacewar kuɗin ne lokacin da kotu ta yi ƙoƙarin cire wani bangare na kuɗin, a nan ne ta gano cewa Naira miliyan 9 kacal ya rage a cikin asusun.

An ruwaito cewa bayan kafa kwamitin binciken, an sace wasu kwamfutoci daga hukumar don neman binne wannan ta’asa.

Muƙaddashin shugaban Hukumar karbar Ƙorafe-Ƙorafe da Cin Hanci da Rashawa ta Jihar Kano, Barista Mahmud Balarabe, ya ce sun gayyaci duk waɗanda ke da hannu da kuma jami’an bankin don yi musu tambayoyi.

An wallafa wannan Labari September 14, 2021 5:59 AM