An Kammala Cinikin Sayar Da Chelsea Ta Ingila

Ana gab da shiga wani sabon tarihi a duniyar kwallon kafa, yayin da aka kammala hada hadar sayar da shahararriyar kungiyar kwallon kafar Ingila din nan ta Chelsea, wadda sayar da ita ya biyo bayan takunkumin da aka kakaba ma mamallakinta mai barin gado, saboda alakarsa da Shugaba Vladimir Putin.