SHUGABAN ƘASA 2023: Jonathan ya ƙaurace wa dandalin tantance ‘yan takarar APC

Jam’iyyar APC mai mulki ta fara aikin tantance ‘yan takarar shugaban ƙasa, bayan tsaiko na makonni biyu da aka samu.
A yanzu haka dai ana tantancewar a otal ɗin Hilton, Abuja.
Tun da farko dai an tsara za a yi aikin tantancewar a ranakun 14-15 Ga Mayu, amma sai aka ɗaga zuwa ranar 23 Ga Mayu.
Daga nan kuma an sake ɗagawa zuwa 29 da 30 Ga Mayu, yayin da kuma aka ɗaya Gangamin Zaɓen Takarar Shugaban Ƙasa zuwa 6 zuwa 8 Ga Mayu.
Duk da an hana ‘yan jarida shiga zauren tantancewar, an ruwaito cewa za a tantance ‘yan takara ne su 23, ciki har da Bola Tinubu da Mataimakin Shugaban Ƙasa, Yemi Osinbajo da kuma Rotimi Amaechi.
Yayin da Jonathan ya ƙi karɓar fam ɗin da wata ƙungiya ta ce ta sai masa, hukuncin da Babbar Kotun Tarayya ta yanke shi ne Jonathan na da ‘yancin sake tsayawa takara a zaɓen 2023.
Sai dai kuma yayin da ake tantance ‘yan takarar APC a yau Litinin a Abuja, har yanzu ba a ga wulgawa ko giftawar Jonathan a wurin tantancewar ba.
A halin yanzu dai Jonathan ya na ƙasar Italiya wurin taron Ƙungiyar haɗin guiwar Afrika da Gabas ta Tsakiya.