IDAN LAILA TA ƘIYA A KOMA BASHA: Yadda Bala Gwamnan Bauchi ya haɗa takarar shugaban ƙasa da takarar gwamna a lokaci ɗaya

Sakataren Gwamnatin Jihar Bauchi Ibrahim Kashim ya lashe takarar Gwamna a ƙarƙashin PDP a jihar, a ranar Laraba.
Sai dai kuma Kashim ya shiga takarar ce a matsayin ɗan-koren Gwamna Bala Mohammed, wanda nan ba da daɗewa ba Bala zai karɓi takarar daga hannun sa, tunda ya sha kaye a takarar fidda gwani na shugaban ƙasa a ƙarƙashin PDP, a ranar Asabar a Abuja.
Kashim dai ya ci takarar babu hamayya, a wani taron da aka yi wanda har gwamnan ya halarta, shi da mataimakin sa Bana Tela.
Kashim ya zama Sakataren Gwamnatin Tarayya cikin Yuni, 2021, ya zama mutum na farko da ya ci zaɓen fidda-gwani salum-alum, ba tare da ya fito ya bayyana cewa zai yi takara ba. Kai ko hoton sa ma ba a liƙa a fasta ko jikin bango ba.
Majiya ta ce Gwamna Bala Mohammed ya amince masa ne saboda amanar da ke tsakanin su.
Shi dai Bala ya samu ƙuri’u 20 ne kacal a zaɓen fidda gwani na shugaban ƙasa a PDP.
Ɗan Takara Ɗaya Tilo: Duk da cewa duk an san ƙulle-ƙullen da Bala ya yi wajen ɗora ɗan-koren sa takarar gwamna a zaɓen fidda gwani, deliget sun cika Zaranda Hotel na Bauchi, inda aka shirya yin zaɓen fidda gwani.
Wakilan zaɓen sun jefa masa ƙuri’u 656, sai ƙwaya ɗaya tal ce ba a dangwala daidai ba.
Baturen Zaɓe ya bayyana cewa, “A bisa ƙarfin ikon da doka ta ba ni ta jam’iyyar PDP, ina mai bayyana Barista Kashim Ibrahim a matsayin ɗan takarar gwamnan Bauchi a zaɓen 2023.”
Bayan Kashim ya yi bayanin murnar lashe zaɓen fidda gwani, ya yi dogon jawabin godiya tare da cewa zai yi ƙoƙarin ganin ya lashe zaɓen gwamna a cikin 2023.
To sai dai kuma duk ana ganin cewa Kashim ɗan-kore ne, nan ba da daɗewa ba zai damƙa wa Gwamna Bala Mohammed takarar sa.
Dokar Najeriya Ce Ta Bai Wa Gwamna Bala Damar Yin Wannan Shirbicin:
Sashe Na 35 Na Dokar Zaɓen Najeriya ya bada damar ɗan takara ya tura ɗan-koren sa ya yi masa takara kamar haka:
“Ɗan takara zai iya janyewa daga takarar da ya yi nasara a zaɓen fidda gwani. Zai janye ne ta hanyar rubuta wa jam’iyyar sa wasiƙar janyewa mai ɗauke da sa hannun sa.
“Daga nan kuma ita jam’iyyar da ta tsayar da shi ɗin za ta aika da sanarwar ta sa zuwa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC). Amma ya kasance an sanar wa Hukumar Zaɓe ta Ƙasa kafin a kai ga saura kwanaki 45 a yi zaɓen da ya janye tsayawa takarar.”
Ba Gwamna Bala Mohammed ne ya fara yin haka ba. Gwamna Aminu Tambuwal na Sokoto ya yi haka a 2019, lokacin da ya fito takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin PDP.
Shi ma Bukola Saraki ya taɓa yin haka cikin 2019 a takarar Sanatan da ya tura ɗan-kore, lokacin da Saraki ɗin ya fito takarar shugabancin ƙasa a ƙarƙashin PDP.