An kama Sanata Ekweremadu da matar sa a Landan, bisa zargin yunƙurin cire ƙodar wani ƙaramin yaro

Mai Shari’a na Kotun Majistare da ke Uxbridge a birnin Landan ya hana belin tsohon Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa ta Najeriya, Ike Ekweremadu a ranar Laraba.
‘Yan Sandan Birnin Landan ne su ka damƙe shi tare da maka shi kotu, bayan sun zarge shi da ɗibga harƙallar safarar wani ƙaramin yaro zuwa Ingila da nufin cire ƙodar sa.
Tun da farko dai an kama Ekweremadu shi da matar sa ne a ranar Alhamis, tare da cajin su da laifin haɗa baki cikin harƙallar shiga Ingila da ƙaramin yaro da su ka ce shekarun sa 20, alhali bai wuce 15 ba.
Ana cajin su da laifin shiga da ƙaramin yaro cikin Ingila ɗan shekaru 15 daga Najeriya, wanda su ka yi iƙirarin cewa za a samar masa rayuwa mai kyau a Ingila, amma a bayan fage Ekweremadu ya yi niyyar kai yaron ne a cire masa ƙoda, shi yaron bai sani ba.
Masu gabatar da ƙara sun shaida wa kotu cewa a cikin fasfo na yaron, Ekweremadu ya yi ƙaryar cewa shekarun yaron 21. Amma magana ta gaskiya, masu bincike sun bankaɗo cewa shekarun yaron 15 kacal.
Masu gabatar da ƙara sun shaida wa kotun cewa Ekweremadu da matar sa na da wata ‘ya wadda ta daɗe ta na kwance, ta na fama da ciwon ƙoda, har ana yi mata gashin ƙoda (dialysis).
Sun ƙara da cewa sun haƙƙaƙe cewa Ekweremadu da matar sa sun shiga Landan da yaron ne domin a ciri ƙodar sa a dasa wa ‘yar su Ekweremadu.
Ekweremadu da matar su dai kowane ya ɗauki lauyan da ke kare shi daban. Sun roƙi kotu ta sake su, amma Mai Shari’a ya ce ba maganar sakin su tukunna. Su biyun dai sun damƙa wa Gwamnatin Birtaniya fasfo ɗin su.
PREMIUM TIMES ta samu wata tsohuwar wasiƙar da Ekweremadu ya aika wa Ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Najeriya, inda ya sanar da shi neman biyar wani namiji.
A cikin wasiƙar, Ekweremadu ya shaida wa ofishin cewa zai kai yaron ne Landan domin a yi masa maganin da ka iya zama dashen ƙoda, ko ya bayar da ƙodar sa a dasa wa wata yarinya mai suna Sonia.
Ya ce za a yi dashen a Asibitin Royal Free Hospital da ke Landan.
Wasiƙar ba ta bayyana adadin shekarun yaron ba, amma dai masu gabatar da ƙara sun shaida wa Mai Shari’a cewa Ekweremadu ya yi wa yaron ƙarin shekaru, daga 15 ɗin ainihi na yaron zuwa shekaru 21.
Mai Shari’a ya bada umarnin a tsare Ekweremadu da matar sa har zuwa ranar 7 Ga Yuli, ranar da za a ci gaba da sauraren ƙarar.