Inganta Rayuwar Matasa Ta Hanyar Wasan Kwallon Kafa Da Gudunmawar Al’Ummah A Jigawa, Ahmed Ilallah

Wani abu da ya ja hankali na a kan wannan batu shine, yunkurin da wasu matasa suka yi min da na zo dan zama jagoran shugabannin kungiyar su ta kwallon kafa, sai na nuna musu a’a ganin cewar ni bani da kwarewa dama cikakken nazari a kan al’amuran da suka shafi wasanni musamman na grass root (kasa-kasa), kawai ni dai ina da sha’awar wasannin da kuma burin yadda wassani, musamman kwllon kafa zai taimakawa rayuwar matasan mu, domin shi suka fi maida hankali a kai.

Karamin bincike da nazarin da nayi ne musamman a kan cigaban wasan kwallon kafa naga ya kamata muyi tsokaci a kai don muhimmancin rayuwar matasan mu da kuma dacewar masu hali su shigo ton tallafawa wasanni a jahar mu. Domin duk inda aka samu cigaba a harkar matasa to al’umar su sun tallafa musu.

Wani abin mamaki da ban sha’awa shine yadda naga kana nan clubs wato kungiyoyi na unguwanni suna sabanta yarjejeniya ta saya da sayarwa ýan wasa, da ma ba da aron ýan wasa transfer market, wand a da hatta wasanni a tsakanin wadan nan kungiyoyi ba a cike wanye wa lafiya ba. Nazari ya nuna cewa wanan cigaba yazo ne bayan da da shi Hussaini Rally ya assasa da daukan nauyin lague a kannan hukumomin jigawa ta gabas da wasu daga cikin kananan hukumomi a sauran yan kunan Jigawa.

Nazari da bincike ya nuna a kwai a kalla kimanin kungiyoyi (clubs) sama da 150 na matasa da suke fafatawa a wasanin league.

A yanzu ma Kanan hukumomin Guri, Auyo, K/Hausa, K/Kasamma, Birniwa da Hadejia duka suna fafatawa a gasar primier da ya assasa, a kalla kowace karamar hukuma a kwai clubs 20 da suke wannan gasa, tunanin wadannan wasanni ba kawai motsa wasan kwalo bane harma da taimakon matasan don samun rayuwa mai inganci.

A yanzu ma Kanan hukumomin Guri, Auyo, K/Hausa, K/Kasamma, Birniwa da Hadejia duka suna fafatawa a gasar primier da ya assasa, a kalla kowace karamar hukuma a kwai clubs 20 da suke wannan gasa, tunanin wadannan wasanni ba kawai motsa wasan kwalo bane harma da taimakon matasan don samun rayuwa mai inganci.

A karamar hukumar Hadejiakadai ana gasar wasanni guda hudu, clubs 28 ne suke fafatawa a gasar professional league, 20 suke buga premiere league, clubs 22 suke buga League 1 sannan kuma clubs 26 suke fafatawa a gasar league 11. Wannan wasanni ya kara zaman lafiya da zumunta a tsakanin mutanen wannan yankin.

A bin mamaki tsarin da ake league kamar a Karamar Hukumar Hadejia tamkar a kasashen turawa, a kwai rukunin da suke buga Premier League, Nationwide I & II, wannan ya dawo da tarbiyar wassan kwallo a tsakanin matasan mu, ya kuma bude hanyar dorewa da wasan kwallo ya zama sana’a atsakanin matasan mu.

Bincike ya nuna wasu da ga cikin matasan a yau suna buga kwallo a manyan kungiyoyin kwallo na Nigeria a matsayin professionals, wasu ma sun zaman to coache wato masu horaswa, wasu kuma sun zama kwararrun alkalan wasa, wannan kadai ba karamin dan ba bane wajen farkar da al’umma da shugabanni cewar za’a iya tallafawa matasa don samun sana’a ta hanyar wasannin.

A bin sha’awa ma shine yadda yawan wasanni da kuma tsarin da a ka saka na cigaban wasanni a yau, ya taimaka gaya wajen chanjawa matasan mu tunani a kan ta’ammali da miyagun kwayoyi, karamin bincke a tsakanin matasan mu ya nuna cewa, wasannnin da matasa suke fafatawa a kai, ya zama dole sai matasa suna kykkyawan atasaye da cikekkeyir lafiya in har matashi ya na son nuna bajintar sa da kuma cika burin san a zama kwararren dan kwallon kafa. Yawan wasanni ya sanya matasa barin ta’ammali da miyagun kwayoyi da kuma hikimar yakar maye ta hanyar wasanni.

Karatun matasa, wani abu da Hussaini ya kawo a shigar sa alámarin kwallon kafa shine, wajen maida matasa da yawa makaratu domin su ci gaba da karatun su, yayi haka ne wajen basu kyawawan shawara da maida su makarantu, basu kwarin gwiwa dama tallafa musu.

A cigaban wasan kwallon kafa a Jigawa, kungiyar da Hussaini Rally ya assasa ta HALFA sama da shekaru uku wannan kungiyar tana daga cikin kungiyoyin da suke buga wasanni kwararru a Nijeriya wato professional league, wato Nigerian Nationwide League.

Wasu yan wasa daga cikin wannan kungiyar a yau suna bugawa manyan kungiyoyi a Nijeriya, wasu ma fafutukar fita kasashen waje, wannan ba karamin ci gaba a ka samu ba a harkar wasanni ba a Jigawa ba.

[email protected]