Wani Sanatan Zamfara ya sanar da ficewa daga PDP a zauren majalisa

Raba a Facebook

Tura zuwa Twitter

Sanata mai wakiltar Zamfara ta Tsakiya a majalisar dattawa ta ƙasa, Sanata Hassan Muhammed Nasiha, ya sanar da ficewar sa daga jam’iyyar PDP.

Ɗan majalisar ya sanar da murabus ɗin nasa ne a cikin wata wasika da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan ya karanta a zauren majalisar a yayin zaman yau Talata.

Ya ce ya yanke shawarar ficewa daga PDP ya zama dole duba da yadda jam’iyyar PDP ke neman ruguje bisa rikicin cikin gida da wariyar da ake nunawa reshen jihar PDP jihar ta Zamfara.

Sanata Muhammed, a cikin wasikar, bai bayyana jam’iyyar da zai shiga ba.

Yana daga cikin ‘yan majalisar daga jihar Zamfara da ake sa ran za su bi gwamnan jihar, Bello Muhammad Matawalle zuwa jam’iyyar APC.