An fara kama Kwarababbun motoci a Abuja, duk za markade su sannan a kai masu shi gaban hukuma

Hukumar kula da rajistar motoci dake Babban Birnin Tarayya Abuja ta bayyana cewa zuwa yanzu ta kama Kwarababbun motoci 20, Keke Napep 10 da babura 15 ranar Talata.
Hukumar ta ce wadannan ababen hawan za a markade su sannan za a kai masu su kotu.
Shugaban aiyukka na hukumar Deborah Osho ta sanar da haka.
Deborah ta ce za a kai masu Kwarababbun ababen hawan kotu bisa ga laifukan da suka hada da amfani da lalataccen abin hawa, tsayawa a wuraren da aka hana tsaya wa da shiga wasu wurare da unguwannin da aka irin wadannan motoci shiga.
Ta ce hukumar ta kama wadannan ababen hawan ne domin tsaftace Babban Birnin Tarayyar.
Deborah ta Yi kira ga masu ababen hawa na haya da su tabbatar sun kiyaye dokokin amfani da ababen hawa da na haya domin guje wa afkawa cikin matsaloli irin haka.
Shugaban askarawan dake kama motoci da ababaen hawa da ba su da kyan aiki a cikin garin Abuja Peter Olumuji ya ce abinda ake yi yanzu zai sa a samu tsaro a fadin Abuja.
Idan ba a manta ba, sabon ministan Abuja, Nyesome Wike ya gargadi duk masu irin wannan motoci, da wasu harkalla da ake gudanarwa a Abuja ciwa zamanin su ya wuce. Yanzu Gyara ya zo kuma gyra za a yia babban birnin.