Jabun maganin Maleriya ya karade kasar nan – Majalisar Tarayya

Kwamitin dakile yaduwar cututtukan kanjamau, tarin fuka da zazzabin cizon sauro na majalisar wakilai ta kasa ta yi kira ga gwamnatin tarayya kan daukan matakan da suka fi dacewa domin hana jabun magungunan cizon sauro a kasar nan.

Shugaban kwamitin Amobi Ogah mai wakiltan jihar Abia daga jami’yyar LP ya sanar da haka a Wani takarda da ya fitar domin tunawa da ranar Cutar zazzabin cizon sauro ta duniya da aka yi ranar Lahadi.

An kebe ranar 20 ga Agusta na kowace shekara bayan wani Bature Ronald Ross ya gano cewa macen sauro ‘Anopheline’ ne ke yada cutar bayan ta ciji mutum.

Taken taron bana shine “Yakar cutar da ta fi kisan mutane a duniya wato sauro”.

Majalisar ta ce ya zama dole gwamnati ta yi gaggawar daukan tsauraran matakai domin dakile yaduwar cutar musamman yadda Najeriya na daga cikin kasashen duniya dake da yawan mutane da cutar ke hallakawa.

“Za mu yi kokari wajen ganin an hana jabun maganin cutar sannan za mu karfafa cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko domin ganin sun dakile yaduwar cutar a kasar nan.

“Adadin yawan mutanen da cutar ta kashe a Najeriya ya Kai kashi uku na mutum 619,000 da cutar ta kashe a duniya.

Ogah ya ce kwamitin a shirye yake domin hada hannu da kungiyoyi da masu ruwa da tsaki domin dakile yaduwar cutar a kasar nan.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ta bayyana cewa masana kimiyyar hada magunguna sun hada maganin rigakafin zazzabin cizon sauro ta farko a duniya.

Shugaban WHO Tedros Ghebreyesus ya ce maganin zai taimaka wajen kare mutane musamman kananan yara daga kamuwa da cutar.