Ɗiyar Ƴar’Adua da Ministan Abuja sun ruƙume a kan wani kantamemen fili a Abuja

Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja ta ƙi amsar roƙon da Zainab Ƴar’Adua ta yi mata, inda ta roƙi kotun ta hana Ministan Babban Birnin Tarayya ko wasu masu iƙirari iko kan filin da su ke shari’a a kan sa.

Zainab ƴar Marigayi Umaru Ƴar’Adua, tsohon Shugaban Najeriya, ta kai ƙara ne da sunan kamfanin ta, Marumza Estate Development Company Limited. Kuma lauyan ta Celestine Hon ne ya shigar da ƙarar.

Zainab ta na iƙirarin cewa katafaren filin nan mai lamba 506 da ke Cadastral Zone B09 a Gundumar Kaso, Abuja, ta ce na ta ne.

Sai dai kuma Hukumar Kula da Babban Birnin Tarayya Abuja, ta ƙwace filin bayan da ta gano cewa ba bisa ƙa’ida aka mallaki filin ba. Wannan mataki da FCDA ta ɗauka ne ya sa Zainab garzayawa kotu, a gaban Mai Shari’a Olukayode Adeniyi.

Mai Shari’a ya ce idan ya hana Ministan Abuja iko kan filin, lamarin zai iya shafar wasu umarni da ya bayar a baya kan filin kenan.

Don haka ya ce duk da iko kan filin ya na hannun Ministan Abuja, ai shari’a daga ƙarshe za ta nuna mai gaskiya.

A kan haka Mai Shari’a ya ce lauyoyin ɓangarorin biyu su gaggauta ganin cewa kotu ta riƙa saurin ganin an kammala shari’ar cikin lokaci.

An dai ɗage sauraren shari’ar zuwa 12, 13 da 15 Ga Oktoba, 2021.

Tushen Rikicin:

Zainab Ɗakingari, matar tsohon Gwamnan Kebbi, Sa’idu Ɗakingari, kuma ‘yar tsohon Shugaban Ƙasa, Marigayi Umaru Musa ‘Yar’Adua ce ta maka Itban Global Resources Limited da mai kamfanin, Halliru Saad Malami kotu.

Zainab ta haɗa da Ministan Abuja da Hukumar FCDA duk ta maka kotu.

Ta ce kantamemen filin dai gudummawa ce aka ba ta shi a ƙarƙashin Dokar Daram-daƙam ta FSCA wadda ba a kankarewa.

A ƙarar Zainab ta shigar a ranar 24 Ga Yuni, 2021, Zainab ta nemi kotu ta ƙwace filin daga Itban a maida wa kamfanin ta wato Marumza.

Sai dai kuma rikici ya ruƙume yayin da Hukumar FCDA ta yi zargin cewa ba bisa ƙa’ida Zainab ta mallaki filin ba.

An yi zargin cewa sunayen daraktocin da ke kan rajistar sunan kamfanin ta Marumza, wato wanda aka yi wa rajista a ranar 5 Ga Yuli, 2009, wato Umar Ibrahim Lange da Maryam Sa’idu, duk sunayen ‘ya’yan ta ne biyu da ta haifa a aure biyu da ta yi na baya. Kuma yaran kowane uban sa daban.

An ce hakan ya saɓa wa dokar CAMA.

Shi kuma Halliru Malami ya yi ƙorafi a kotu a ranar 7 Ga Yuli, 2021, cewa Zainab ta je ta kewaye kantamemen filin da ginin katanga, ba tare da ta sanar da Hukumar FCDA ba.

A yanzu dai sai cikin Oktoba za a fara gwagwagwar shari’a.