AMBALIYAR JIGAWA: Tinubu ya yi tattaki, ya kai gudummawar naira miliyan 50

Ɗan takarar shugaban ƙasa na APC Bola Tinubu, ya yi tattakin zuwa jihar Jigawa a ranar Talata, inda ya kai gudummawar naira miliyan 50 ga waɗanda ambaliyar ruwa ta yi wa ta’adi a faɗin jihar.
Gwamna Abubakar Badaru ne da Sarkin Haɗejia Abubakar-Maje su ka tarbi Tinubu.
Tinubu ya kai ziyarar daidai lokacin da jama’a da dama ke yin tir da Gwamna Badaru, saboda bai je ya yi jaje ga waɗanda ambaliya ya yi wa ɓarna ba, sai dai ya tura wakili kaɗai.
Daidai lokacin ne kuma ɗan takarar gwamnan PDP a Jigawa ya fatattaki Gwamna Badaru saboda watsi da waɗanda ambaliya ya yi wa ta’adi.
Ɗan takarar gwamnan Jihar Jigawa na PDP ya ragargaji Gwamna Badaru Abubakar, saboda watsi da ya yi da waɗanda ambaliya ta yi wa mummunar ɓarna a jihar.
Mustapha Lamiɗo ya ce kamata ya yi Badaru ya je ya yi masu jaje da ta’aziyya, ba wai kawai ya aika masu da saƙon taya su jimami ba.
Yankunan da ambaliya ya fi yi wa mumnunar ɓarna sun haɗa da Dutse, Hadejia da Ringim inda ruwa ya cinye garuruwa da dama kuma ya karya gadoji masu yawa.
Ɗaruruwan mutane a yanzu haka sun yi gudun hijira tare da dabbobin su a wasu garuruwa cikin jihar.
Al’ummar jihar da dama na ci gaba da yin Allah-wadai da halin Gwamna Badaru, wanda aka yi masa shaidar cewa bai damu da zuwa cikin jama’ar da wani Ibtila’i ya shafa ya na yi masu jaje ba.
Mustapha Lamiɗo ya yi kira ga Gwamna Badaru ya gaggauta zuwa ƙauyen Karnaya domin ya ga irin ɓarnar da ambaliya ya yi a garin.
Ya ce zuwan gwamna zai sa ya gani kuma ya ji a jikin sa irin halin rayuwar ƙuncin da jama’ar garin ke ciki.
“Wannan ba lokacin da Gwamna zai turo wakili ba ne, ya kamata ya je da kan sa domin ya gani da idon sa.”
Mustapha Lamiɗo ya bada gudummawa ta naira miliyan 1.4 ga waɗanda ruwa ya yi wa ɓarna a Ƙaramar Hukumar Dutse da Gwaram. Kuma ya yi alwashin nemi masu tallafi domin rage masu raɗaɗin halin ƙuncin da su ke ciki.
Shi kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na APC, Bola Tinubu, ya bayar da gudunmawar naira miliyan 50 ga waɗanda ambaliya ya yi wa ta’adi a jihar Jigawa.
Tinubu ya ce ya je Jigawa ne a ranar Talata domin ya yi wa al’ummar jihar jajen ambaliya.
Waɗanda su ka raka Tinubu sun haɗa da Gwamna Simon Lalong na Filato, Shugaban APC na Ƙasa Abdullahi Adamu, tsohon Shugaban EFCC, Nuhu Ribadu. Gwamna Badaru da Sarkin Haɗejia Adamu Abubakar-Maje ne su ka tarbe su.
Jama’a Na Cikin Halin Ƙunci -Sarkin Haɗejia:
Sarkin ya gode wa ɗan takarar shugaban ƙasa Bola Tinubu, saboda gudummawar da ya bayar, kuma ya roƙe shi ya ƙarasa zuwa Masarautar Hadejia, inda bai taɓa zuwa ba ko sau ɗaya.
Ya ce kuɗin da Tinubu ya bayar za a raba su ne ga yankunan masarautun jihar biyar domin bai wa dukkan waɗanda ambaliya ta shafa.
“Mu na kuma kira ga Gwamna ya ƙara samo wa masu fama da wannan ambaliya tallafi, saboda su na cikin halin ƙuncin rayuwa.”