KORONA: Mutum 103 sun kamu, 6 sun mutu a jihar Adamawa

A cigaba da ƴaduwar Korona a Najeriya, jihar Adamawa ta samu mutum 103 da suka kamu da cutar cikin kwanaki biyar.

Cikin waɗanda suka kamu, akwai mutum 6 da suka rasu.

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC ta bayyana cewa mutum 285 sun kamu da cutar a Najeriya daga ranar 6 zuwa 7 ga Satumba.

Alkaluman yaduwar cutar da NCDC ta fitar sun nuna akwai jihohi da dama da ba su yin hubbasar ganin mutane sun kiyaye dikokin korona sun bari cutar na cigaba da yaduwa kamar wutar daji.

Zuwa yanzu mutum 264,299 ne suka kamu da cutar kuma cutar ta yi ajalin mutum 3,154.

Mutum 3,356 na dauke da cutar sannan mutum 257,629 sun warke a Najeriya.

Yaduwar cutar a Najeriya

Mutum 90 ne suka kamu da cutar a jihar Legas sannan kuma jihar ce cutar ta fi yaduwa a cikin jihohin kasar nan.

Daga jihar sai jihar Adamawa -103, Rivers -46, Delta -33, Kano -8 da Gone -3, Filato-1 da Ekiti-1.

Allurar rigakafin korona a Najeriya

Daya daga cikin hanyoyin guje wa kamuwa da cutar korona ita ce allurar rigakafi.

A dalilin haka gwamnati ke kira ga mutane da su garzaya su yi allurar rigakafin cutar domin samun kariya.

Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta ƙasa NPHCDA ta bayyana ranar Alhamis cewa mutum 32,245,289 sun yi allurar rigakafin korona a kasar nan.

NPHCDA ta ce akwai mutum 12,784,289 da basu kammala yin allurar rigakafin ba a kasar nan.