ƘUNCIN RAYUWA: Doya ta gagari mutanen Enugu, sun koma yi wa dankali cin hannu-baka-hannu-ƙwarya

Wasu mazauna Enugu sun koma cin dankali ganin yadda farashin doya ya cilla sama, ya gagari nauyin aljihun su.

Wakilin NAN da ya karaɗe yawancin manyan kasuwannin Enugu a ranar Asabar da ta gabata, ya lura da cewa dankalin Turawa ya cika kusan dukkanin shagunan da ke sayar da doya.

Wasu masu sayar da doya mai tarin yawa, sun daina sayar da ita saboda tsada, sun koma sayar da dankali, domin yanzu shi ake saye, duk an ƙaurace wa doya.

Yayin da ake sayar da buhun dankali sukutum naira 7,000 zuwa naira 8,500, ita kuma saiwar doya 12 ana sayar da ita naira 6,400 har zuwa naira 7,000.

Yayin da ake sayar da tsaka-tsakiyar doya ɗaya naira 800, ana sayar da ɗan ƙaramin kwanon awo cike da dankali naira 200.

Wasu da aka tattauna da su, sun ce ai dankali ya yaye wa gidaje da dama ƙuncin rayuwa sakamakon tsadar doya.

Wani mai suna Uju Ufondu ya ce “aƙalla idan ka na da naira 500, za ka sayo dankali mai tarin yawa. Duk irin yadda aka sarrafa maka shi kuma za ku ci ku ƙoshi har ku sha ruwa.”

Ita kuwa Vivian Oba cewa ta yi ta dakatar da cin doya ta koma cin dankalin Turawa, saboda doya ta yi tsada. Dama kuma dankali ya fi doya sinadaran gina jiki.”

Wasu masu sayar da dankali sun shaida cewa farashin dankali ya yi arha sosai ne a yanzu saboda lokacin da ne. Ita kuwa doya lokacin ta ya wuce.

“Na daina sayar da doya, yanzu dankali na ke sayarwa. Saboda masu sayen doyar ce su ka daina, su ka koma sayen dankali.”

Ya ce idan bai koma sayar da doya ba, zai rasa kwastomomin sa kenan.

Kelvin Egwu da ke sayar da dankali cewa ya yi a kullum farashin doya tashi ya ke yi sama ya na ƙaruwa. “Shi ya sa na yi watsi da cinikin doya, na koma sayar da dankali. Har sai doya ta yi sauƙi kuma ta wadata sannan zan koma sayar da doya.” Inji Egwu.