AMAI DA GUDAWA: Mutum 4,153 sun kamu, 80 sun mutu a cikin kwanaki 30 a Najeriya – NCDC

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta kasa NCDC ta bayyana cewa cutar amai da gudawa ya ci gaba da yaduwa inda jihohin Borno, Yobe da Gombe ke kan gaba wajen fama da cutar a kasar nan.

NCDC ta ce a cikin wata daya mutum 4,153 sun kamu da cutar sannan ta yi ajalin mutum 80 a jihohi 9 a Najeriya.

Wadannan jihohi sune jihar Borno, Yobe, Gombe, Zamfara, Bauchi, Jigawa, Sokoto, Katsina da jihar Adamawa.

Bisa ga rahoton da hukumar ta fitar ya nuna cewa an samu karin kashi 42% na yaduwar cutar a watan Oktoba fiye da mutum 2,428 da suka kamu da cutar a watan Agustan 2022.

Daga farkon shekaran nan zuwa ranar 2 ga Oktoba NCDC ta samu ƙarin mutum 10,745 da ake zargin sun kamu da cutar a jihohi 31 a kasar nan.

Daga cikin yawan mutanen da ake zaton sun kamu da cutar jihar Borno na da mutum 3,663, sannan Yobe- 1,632.

Sauran jihohi kuwa sun hada da Katsina 767, Taraba 675, Cross River 649, Gombe 470, Jigawa 417 da Bauchi 304.

Maza kashi 48% da mata kashi 52% ne suka kamu da cutar a shekaran 2022.

Bayan haka hukumar ta yi kira ga mutane da su rika tsaftace muhallinsu da amfani da tsaftataccen ruwa domin guje was kamuwa da cutar.

Hukumar ta yi kira ga gwamnati da ta samar wa mutane tsaftattacen ruwa tare da wayar musu da kai sanin muhimmancin tsaftace muhalli da amfani da ruwa masu tsafta.

Ga abubuwa 10 dake haddasa barkewar cutar Kwalera

1. Rashin tsafta da barin ƙazanta a gida, musamman abinci da kayan abinci ko kwanukan cin abinci.

2. Zubar da tulin shara da bola aikin unguwanni, wadda ruwan sama ke maida ƙazantar ta s cikin jama’a.

3. Zubar da shara ko bola ko bayan gida a cikin ƙaramu da magudanan ruwa.

4. Yin bayan gida a fili ko a kan bola.

5. Rashin ruwa mai tsafta a cikin al’umma.

6. Ƙarancin asibitocin kula da marasa lafiya a cikin jama’a marasa galihu.

7. Ƙaranci ko rashin magungunan da za a bai wa mai cutar kwalara cikin gaggawa.

8. Matsalar ƙarancin jami’an kiwon lafiya a cikin jama’a.

9. Rashin hanyoyi masu kyau da za a garzaya asibiti da mai cutar amai da gudawa cikin gaggawa.

10. Shan ruwan ƙarama ko kogi, wanda ake zubar da shara, kashin dabbobi da kuma bayan gida.