A CIKIN SHEKARU TAKWAS: Yadda ƙwararrun likitocin Najeriya fiye da 5,000 su ka yi hijira zuwa Ingila

An tabbatar da cewa fiye da ƙwararrun likitoci ‘yan Najeriya 5,000 ne su ka tsallake zuwa Ingila a cikin shekaru takwas.

Tabbacin adadin waɗannan alƙaluma ya fito daga bakin Shugaban Ƙungiyar Likitocin Najeriya (NMA), Uche Rowland, yayin da ya ke jawabi wurin wani taron tattauna ƙarancin likitoci a Najeriya da kuma dalilin yawan ficewar su zuwa ƙasashe, musamman Ingila.

An shirya taron ne a Abuja ranar Laraba, a ƙarƙashin ƙungiyar dRPC.

Najeriya na fama da ƙarancin likitoci ta yadda aƙalla an yi ƙiyasi da kirdadon cewa likita 1 ne ke duba mutum 5,000, saɓanin ƙa’idar da Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta gindiya cewa kada likita 1 ya zarce duba mutum 600 kacal.

Yadda Likitocin Najeriya Ke Tururuwar Zuwa Ingila:

“Cikin 2015 likitoci 233 ne su ka koma Ingila su na aiki. A cikin 2016 kuma likitoci 276 ne. Sai kuma cikin 2017 likitoci 475 su ka yi ƙaura zuwa Ingila su na aiki.

“Cikin 2018 kuwa an tabbatar da tafiyar likitoci 856, sai kuma cikin 2019 har likitoci 1,347 su ka tafi Ingila yin aiki a can.

“Cikin 2020 wasu likitoci 833 su bi hanya zuwa Ingila, sai kuma wasu 932 a cikin 2021.” Haka Rowland ya tabbatar.

Fargabar Ƙwararar Likitocin Najeriya Zuwa Ingila A 2022:

Rowland ya kuma tabbatar da cewa a cikin watanni shida na farkon 2022, ƙwararrun likitocin da aka bai wa horon aikin likita a Najeriya har su 737 ne su ka fice zuwa Ingila.

Ya ce lamarin abin tsoro ne, domin hakan ya nuna cewa adadin yawan waɗanda su ka koma Ingila cikin 2022 zai zarce na kowace shekara, idan aka haɗa da lissafin waɗanda su ka fita daga watan Yuni zuwa Disamba 2022, domin ba a lissafa da su daga ɗin ba.

Rowland ya ce ƙasar Indiya ce ta fi yawan likitoci baƙi a Ingila, sai Pakistan, sai kuma Najeriya wadda ita ce ta uku.

An tabbatar da cewa akwai ƙwararrun likitoci ‘yan a Ingila za su kai 9,976.

Jami’an Lafiya 13,609 Sun Shiga Ingila Daga Najeriya Cikin 2022 -Hukumar Shige-da-ficen Ingila:

Hukumar Kula da Shigar Baƙi Cikin Ingila ta fitar da rahoton cewa aƙalla adadin jami’an lafiya 13,609 aka bai wa lasisin shiga su yi aiki cikin Ingila a cikin 2023.

Hukumar ta ce an bai wa ‘yan Indiya har mutum 43,966 wannan damar.

Dalilin Ficewar Likitocin Najeriya Zuwa Ingila:

Rowland ya ce daga cikin dalilan ficewar akwai yadda gwamnati ba ta ɗaukar batun kiwon lafiya da muhimmanci.

“Kasafin bara Gwamnatin Tarayya ta ware wa fannin lafiya ƙasa da kashi 5% cikin 100% na kasafin kuɗi. Sannan kuma akwai matsalar tsaro, inda ‘yan bindiga ke yawan yin garkuwa da likitoci, ‘yan ta’adda kuma na yawan kashe wasu.”