Kasuwancin zamani na da tasiri a ɗorewar tattalin arziƙin zamani- Shugaban NITDA

An bayyana tsarin kasuwancin zamani a matsayin mahimmin fannin da zai tabbatar da ɗorewar tattalin arziƙin zamani bisa yadda fasahar zamani ta sawwaƙe wa al’umma wurin saya da sayarwa a yanzu.

Darakta Janar na Hukumar Bunƙasa Fasahar Fasahar Sadarwa ta Ƙasa (NITDA) Kashifu Inuwa Abdullahi CCIE ne ya bayyana hakan, yayin da yake gabatar da muhimmin jawabi a wani taron kwana ɗaya da aka shirya wanda wasu Ƙungiyoyin suka shirya don inganta shugabanci mai taken “Inganta Kasuwancin zamani don Tallafawa Matasa da Dogaro da Kai ”, a Babban Birnin Tarayya Abuja.
Da yake gabatar da jawabin, Kashif Abdullahi wanda ya samu wakilcin Mataimakin sa na Musamman Dr Aminu Lawal, ya bayyana cewa yadda fasahar zamani ya samu karɓuwa ya taimaka wa al’umma wurin samun ingantatyun bayanai wanda a sakamakon hakan ya haifar da sauƙin yanayin aiki.
Dr. Aminu Lawal a wurin taro
Abdullahi ya bayyana cewa NITDA tana da shirye-shirye da dama waɗanda suka dace da tsarin kasuwancin zamani.
Ya ce Hukumar Bunƙasa Fasahar Zamani ta horar da matasa sama da 6000 a fannoni da dama da suka haɗa da ƙirƙira a yanar gizo-gizo, tsarin kasuwancin zamani da dai sauransu.
Ya ƙara da cewa a halin yanzu ma, suna gudanar da bada horo ga wasu matasan, waɗanda suka haɗa masu larurar nakasa, mata a fannin Fasahar Sadarwa (ICT) da horar da masu sana’o’i gyaran wayar salula wanda duk ana yin hakan ne da nufin koyar da su yadda za su ƙara bunƙasa samun su ta hanyar fasahar zamani.

Tura Wa Abokai

An wallafa wannan Labari September 22, 2021 3:19 PM