Algeria Da Burkina Faso Sun Yi Kunnen Doki

Washington D.C. — Algeria da Burkina Faso sun tashi da ci 2-2 a wasan da suka kara a Gasar Kofin Nahiyar Afirka ta AFCON da ake yi a Ivory Coast.

Dan wasan Burkina Faso Mohamed Konate ne ya fara zura kwallo a ragar Algeria gab da ana shirin tafiya hutun rabin lokaci.

Sai dai bayan an dawo dga hutun rabin lokaci, dan wasan Algeria Baghdad Bounedjah ya farke kwallon a minti na 51.

A cikin minti na 70 ne kuma Burkina Faso ta sake samun wata damar inda dan wasanta Bertrand Traore ya zura kwallo ta biyu a ragar Algeria ta hanyar bugun fenariti.

Sai dai murna ta koma ciki ga ‘yan wasan Burkina Faso bayan da Bounedjah ya zura kwallo ta biyu a ragarsu.

Hakan ya karawa Algeria kwarin gwiwar samun zuwa zagayen ‘yan 16.

Yanzu dai Burkina Faso ce a saman teburin rukunin D da maki hudu, Algeria na biye da ita da maki biyu.