Najeriya Ta Kai Zagaye Na Biyu A Gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka

Washington DC — Najeriya ta samu shiga zagaye na biyu a gasar Cin Kofin Nahiyar Afirka bayan ta doke Guinea Bissau ci daya da nema a ranar litinin.

Wasan, da shine na uku kuma na karshe a zagaye na farko, ya baiwa tawagar ta Najeriya maki bakwai a teburin Rukunin A.

Najeriya ta zura kwallo ne a minti na 36, bayan da Guinea ta ci gida ta hannun Opa Sangante.

Da wannan sakamakon, Super Eagles ta kare a mataki na biyu a rukunin farko da maki bakwai, yayin da Equatorial Guinea ce ta yi ta ɗaya da maki bakwai iri ɗaya da na Najeriya, sai dai ta fi Najeriya zura kwallaye a gasar.

A dayan wasan Rukunin A Equitorial Guinea ta lallasa Kwaddebuwa, masu karban bakuncin gasar ci 4-0.