Akwai zazzafar Korona dake tafe da tafi Omicron idan… – NCDC

Shugaban hukumar dakile yaduwar cututtuka ta ƙasa NCDC Ifedayo Adetifa ya gargaddi ‘yan Najeriya da su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar korona cewa rashin yin haka ka iya sa a samu bullowar zazzafan sumfurin korona.

Adetifa ya ce za a iya shiga cikin mummunar hadari idan aka yi wasti da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar.

Ya ce bullowar sumfurin Omicron ya zo ne a matsayin tuni ga kasashen duniya cewa har yanzu ba a ci nasaran yaki da korona ba
“Abin godiya ne yadda cutar ba yi mana kisan kiyashi ba a Najeriya amma haka ba shine zai cutar ba zai ci gaba da yaduwa ba ko mutane ba za su kamu da cutar ba.

“Abin dake faruwa shine idan ba mu mai da hankali wajen dakile yaduwar cutar ba, za ta ci gaba da rikida har a samu zazzafar Korona da ta fi wanda suka bulla a baya.

“Muna kira ga mutane da su koma su ci gaba da kiyaye sharuddan gujewa kamuwa da cutar tare da Yung allurar rigakafin korona domin wadannan sune matakan da za su taimaka wajen dakile yaduwar cutar.

Kada a firgita da ‘Omicron’ Rigakafin Korona na magani har yanzu.

Adetifa ya yi magana da kaukkausar murya cewa kada a firgita da sumfurin Omicron domin har yanzu maganin rigakafin na maganin cutar.

Adetifa ya ce har yanzu yin allurar rigakafi na daga cikin matakan samun kariya daga kamuwa da mutuwa daga cutar.

Ya ce koda cutar na da illa ga maganin rikagafi illa da zai yi ba zai kai yadda idan mutum bai yi allurar rigakafi ba.

“Misali idan maganin rigakafi na Samar wa mutum kariyar Kashi 90% daga kamuwa da sumfurin Delta maganin rigakafin zai iya samar wa mutum kariyar Kashi 80% daga kamuwa da sumfurin Omicron.

NCDC ta ce har yanzu dai babu wani rahoton wannan sabuwar cuta ta yi kisa a Najeriya, amma fa an gano sagwangwaman ta har guda 126.

“ Gano sagwangwaman wannan sabuwar cuta tare da gami da fantsamar cutar a Afrika ta Kudu, hakan ya tabbatar da cewa wannan cutar ta na saurin yaɗuwa a cikin mutane.

Abubuwa 7 da NCDC ta sani game da sumfurin Omicron

1 Menene cutar?

Omicron sabuwan nau’in cutar korona ne da aka fi sani da B.11.52g wanda kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO ba ta zaci cewa zai zama abin damuwa ba a duniya

2. Yaushe aka fara gano cutar?

An fara gano wannan nau’in cutar a kasar Botswana ranar 11 ga Nuwanba 2021.

3. Me ya sa cutar ya zama abin damuwa yanzu?

Nau’in Omicron na iya rikida sau 30 wanda ya ninka yawan da nau’in ‘Delta’ zai iya rikida.

4. Yana da saurin yaduwa?

Babu tabbacin ko sumfurin na da saurin yaduwa amma duk da haka a cikin makonni biyu bayan bullowar cutar an samu karuwa a yaduwar korona saboda bullowar sumfurin Omicron.

Shari’o’in darajar RO shine 1.93 na omicron sannan 1.47 na Delta.

5. Maganin rigakafi zai iya kashe kwayoyin cutar?

Omicron sabuwan sumfurin cutar korona ce wanda babu wanda ke da masaniya akanta. Masana kimiya na gudanar da bincike a kan cutar inda bayan sun gano wani abu akan shi a iya bayyana wa mutane.

6. Akwai maganin da ake amfani da shi wajen warkar da mutane?

A halin yanzu oxygen da dexamethasone ne kadai ke ceton rayuwa wadanda suka kamu da cutar amma akwai bayanai da suka nuna cewa akwai maganin rigakafi guda biyu Malnupiravir da Favipiravir da za su iya warkar da mai fama da cutar.

7. Hanyoyin guje wa kamuwa da cutar.

Saka takunkumin fuska, wanke hannu da ruwa da sabulu, nisanta kai da taron mutane da zama a daki ko wurin dake da iska.