RANAR KANJAMAU TA DUNIYA: Nuna wariya da rashin samun magani na cikin dalilan dake sa cutar na yaduwa

Jami’an lafiya sun koka da yadda matsalar nuna wariya ga masu dauke da cutar kanjamau ke dada sa ana samun karuwar yaduwar cutar a duniya.

Jami’an lafiya sun ce kamata ya yi a samu raguwan yaduwar cutar a duniya ganin cewa Hukumar lafiya ta duniya ta yarda a rika amfani da maganin ‘HIV Pre-Exposure Prophylaxis (PrEP)’ wajen samar da kariya ga cutar.

HIV Pre-Exposure Prophylaxis (PrEP) magani ne dake samar wa mutum kariya daga kamuwa da kanjamau.

Bayan wannan magani amfani da kororo roba na taimakawa wajen kare mutum daga kamuwa da cutar.

Sakamakon Bincike ya nuna cewa mutum miliyan 1.9 ne suka kamu da cutar a shekarar 2020.

Binciken ya kuma nuna cewa masu ta’ammali da kwayoyi, karuwai da masu luwadi suka fi kamuwa da kuma yada cutar.

A wata tattaunawa da wakiliyar PREMIUM TIMES ta yi da wata karuwa dake zaune a Karu Abuja mai suna Layla Abah ta ce ta san maganin PrEP wanda ke samar wa mutum kariya daga kamuwa da kanjamau domin ta yi amfani da shi na tsawon watanni shida a shekaran 2017.

Layla ta ce gudun nuna wariya da rasa kwastomomi ya sa ta daina amfani da maganin.

Wani mai ta’ammali da muggan kwayoyi Abdul Ibrahim Shima ya ce gudun nuna wariya ya sa ya ki amfani da maganin. Ya ce ya ki amincewa da maganin ne saboda maganin na kama da wanda masu fama da kanjamau ke amfani da shi.

Bayan haka wani likita dake bada shawara kan amfani da maganin PrEP dake aiki da gidauniyar RISE George Ikaraoha ya ce kamata ya yi a dauki mataki wajen wayar da kan mutane game da illar dake tattare da nuna wa masu fama da kanjamau wariya da samar da kula wa masu fama da cutar a farashi mai sauki.

Ikaraoha ya ce banda nuna wariya tsadar farashi magani da rashin samun magani na cikin matsalolin dake hana a samu nasaran a yaki da cutar.

Yaduwar cutar Kanjamau

Sakamakon binciken da WHO ta fitar ya nuna cewa mutum miliyan 37.7 ne uka kamu da kanjamau a shekaran 2020 a duniya.

Daga cikin wannan yawa akwai yara miliyan 1.8 da suka kamu da cutar.

Binciken ya kara nuna cewa akwai mutum miliyan 6.1 da suke dauke da cutar amma Basu sani ba.

Cutar ta kuma yi ajalin mutum 680,000 a shekaran 2020 a duniya.
Bayan haka sakamakon binciken asusun UNAIDS ya nuna cewa tun bayan bullowar cutar korona akalla mutum miliyan 75.7 ne suka kamu da cutar.

UNIAIDS ta ce kasashen dake tasowa na cikin kasashen da suka fi fama da yaduwar cutar.

A rana mutum 4,500 ne ke kamuwa da cutar inda daga ciki Kashi 59 daga yankin Kudu da Saharan Afrika.

Yammaci da Kudancin Afrika ne suka fi yawan masu fama da cutar a duniya inda a wadannan yankuna mutum miliyan 20.7 ne ke dauke da cutar
A shekaran 2019 mutum 730,000 ne suka kamu da cutar a wadannan yankuna.

Ranar cutar kanjamau ta duniya rana ce da aka kebe domin tunawa da wadanda suka kamu da cutar da wadanda cutar ta kashe a duniya.

Rana ce Kuma da ake wayar da kan mutane mahimmancin yin gwajin cutar, hanyoyin samun kariya daga kamuwa da cutar da wayar da kan mutane game da matsalolin nunawa masu fama da cutar wariya.

A takaice dai an kebe wannan rana domin dakile yaduwar cutar a duniya.