Akwai cinkoson ƙararraki 128,000 a gaban Alƙalan Babbar Kotun Tarayya 75 -Shugaban Alƙalai

Shugaban Alƙalan Babbar Kotun Tarayya, Mai Shari’a John Tsoho, ya bayyana cewa akwai tulin shari’u har 128,234 da ke gaban alƙalai 75 na Babbar Kotun Tarayya (Federal High Courts).

John Tsoho ya yi wannan bayani a lokacin da ya ke nuna tsananin damuwar sa kan tulin shari’un da ke gaban ‘yan ƙalilan ɗin manyan alƙalai 75 kacal da ake da su a manyan kotuna.

Idan akwai shari’u 128,000 a gaban masu shari’a 75, to hakan na nufin duk mai shari’a ɗaya akwai shari’u 1,700 a gaban sa masu jiran a yanke hukunci kan su.

Tsoho ya yi bayanin a lokacin da ya ke buɗe taron sabon zangon shari’a na shekarar 2021/2022 a Abuja.

Ya ce masu shari’a a Kotun Daukaka Ƙararraki sun samu tulin shari’un ne mafi yawa tun bayan komawa aiki bayan dogon hutun korana da ma’aikatan gwamnati, ciki har da masu shari’a su ka yi.

Ya ce zangon shari’un 2020)2021 ya fara daga Satumba, 2020 zuwa Yuni, 2021, aka rufe a Yuli, 2021.

Tsoho ya ce daga Satumba 2020 zuwa Yuni 2021, an shigar da ƙararraki guda 8,309 a Manyan Kotunan Tarayya.

A yanzu akwai shari’u 40,822 waɗanda na rikice-rikice ne, sai kuma na manyan laifuka guda 197, sai kuma 35,563 na neman umarnin kotu, sannan kuma akwai 20,258 waɗanda roƙo ne ga kotu ta tilasta bin wani umarni ko neman haƙƙin waɗanda aka tauye wa haƙƙi.

“A cikin shekara ɗaya an yanke hukuci 6,915 a Kotunan Tarayya ƙarƙashin alƙalai 75, sannan akwai kwantai na shari’u har 128,234.” Inji Tsoho.

Tsoho ya ce alƙalan da za a ɗauka a Babbar Kotun Tarayya kwanan nan za su kawo raguwar cinkoson shari’u sosai.