TATSUNIYA KO TARON TSIYA: APC ta zame wa ƴan Najeriya takalmin kaza, PDP ba za ta iya karawa da mu ba a 2023 – In ji APC

Kakakin jam’iyyar APC na rikon kaura, John Akpanudoedehe gargaɗi ƴan Najeriya kada su biye wa ruɗin PDP na wai sune za su dawo su gyara Najeriya.

Mun ji wai sabon shugaban jam’iyyar PDP Iyorchia Ayu na cewa wai APC ta taliyar ƙarshe ne daga wannan karo, wai ƴan Najeriya za su wancakalar da ita a 2023.

” Toh ya sani cewa ƴan Najeriya da kan su ba za su yi kuskuren dawo da PDP kasarnan ba.

” Duk da ɗaukan nauyin rikice-rikice da Jam’iyyar PDP keyi, a cikin wannan yanayi mun yi nasara a kan PDP kuma haka za mu ci gaba da yin Nasara akan PDP domin ƴan Najeriya ba su tare da ita.

“Kawai don shugaban Kasa ba mai surutu bane, amma ba a raɓa fiddo wani shiri ko tsari a kasarnan don taimakon talakawa kamar yadda Buhari yayi ba. Na kalubalanci koma waye, babu wannan gwamnati idan ba gwamnatin Buhari ba.

” Matasa na jin alat, mata na jin alat, manoma na jin alat, ma’aikata ma ba a barsu a baya ba, suma suna jin alat akai-akai sannan kuma ga tallafin Korona da ake ta raba wa talakawa suna morewa.

” Idan maganan rashin tsaro ne, kowa ya sani a zamanin PDP akwai kananan hukumomin da kwata-kwata ta koma ƙarƙashin ikon ƴan ta’adda ne, amma yanzu babu ko daya saboda jajircewar gwamnatin APC.

A karshe yayi watsi da rade-radin da ake yaɗawa wai wasu sun canja shugabancin APC na rikon kwarya, wannan ba gaskiya bane, APC na dau daure tamau bata girgiza.