Kotu ta yanke wa mutumin da ya yi wa ‘yar shekara 17 fyade hukuncin daurin rai da rai

Kotun dake sauraren kararrakin fyade da cin zarafin mata da yara kanana dake Ikeja jihar Legas ta yanke wa Isiaka Adeoye da ya yi wa ‘yar shekara 17 fyade a gona hukuncin daurin rai da rai.
Alkalin kotun Abiola Soladoye ya yanke wannan hukunci bayan hujjoji, shaidu da sakamakon gwaje-gwajen asibiti da aka gabatar a kotun sun tabbatar Adeoye ya aikata hakan.
Lauyoyin da suka shigar da karar Olusola Soneye da Ms Abimbola Abolade sun bayyana cewa Adeoye ya danne yarinyar ranar 22 ga Janairun 2020 a gonar sa dake rukunin gidajen Graceland dake Idimu.
Lauyoyin sun ce a wannan rana mahaifiyar yarinyar ta aike ta zuwa gona ta debo ruwa sai dai da yarinyar ta je gonar sai Adeoye wanda shi ma’aikaci ne a gonar ya aiki ta kuma.
” Da yarinyar ta dawo daga aiken sai ta iske Adeoye ya yi mankasa da giya sannan azakarinsa ya mike kuma ya saka mata kororo roba.
“Adeoye ya yi wa yarinyar diran mikiya inda kafin ta ankare ya yi mata fyade.
“Sakamakon gwajin da aka yi wa yarinyar da shaidu uku tare da bayanin da yarinyar ta bayar a kotu duk sun tabbatar cewa Adeoye ya yi mata fyade.
Alkali Soladoye ya ga laifin yarinyar da bata gudu a lokacin da ta ga azakarin Adeoye a mike sannan har ta tsaya ya kamata ta ya danne ta.
Akarshe sai ya yanke hukuncin daurin rai da rai ga Adeolu.