AfCFTA: Ghana Zata Karbi Bakuncin Shugabannin Afirka 12 Da Manyan ‘Yan Kasuwa A Taron Harkokin Cinikayyar Afrika

A karkashin jagorancin shugaban Ghana Nana Akufo-Addo, da babban sakataren harkokin cinikayya tsakanin kasashen Afirka (AfCFTA) Wamkele Mene za a yi taron kan ci gaban Afirka karo na farko a Ghana. Taron da masu ruwa da tsaki suka ce Ghana da Afirka baki daya, za su amfana da shi.