2023: Rundunar Tinubu ta yi babban kamu a bangaren watsa labarai, ta cafke zaratan ƴan jarida, Jega da AbdulAziz

A ci gaba da faɗaɗa ɓangaren watsa labarai da hulɗa da jama’a da rundunar Kamfen ɗin Tinubu ke yi ta naɗa fitaccen ɗan jarida Mahmud Jega babban mai ba da shawara, shikuma AbdulAziz AbdulAziz mataimaki na musamman dukkan su kan harkokin yaɗa labarai.
A sanarwar haka da wanda Tunde Rahaman ya saka wa hannu, ya ce dukkan su za su fara aiki me nan take.
An naɗa Mahmud Jega babban mai bada shawara kan harkokin hulda da jama’a ga kamfen ɗin Tinubu sai kyma AbdulAziz AbdulAziz babban mai taimakawa wajen harkokin yaɗa labarai da hulda da jama’a.
Wannan babban ci gaba ne aka samu ga tafiyar rundunar Tinubu musamman a yankin Arewa.
Jega da AbdulAziz fitattun ƴan jarida ne wanda suka yi fice a harkar jarida.
Jega kwararren mai yin dharhi ne kuma tsohin mataimakin shugaban jaridar Daily Trust. Sannan kuma shine mawallafin jaridar 21st Chronicles.
Dukkan su za su yi aiki ne musamman don yankin Arewa da mutanen yankin ta hanyar tallata ɗan takarar shugaban Kasa na APC Bola Tinubu a yankin ya ci gaba da samun karbuwa.
Tinubu, Atiku, Kwankwaso da Obi ne ke kan gaba wajen ganin ɗayan su ya ɗare kujerar shugabancin Najeriya bayan wa’adin Buhari ya cika a watan Mayu.
Tinubu da ɗan asalin yankin kudancin Najeriya ne na bukatan zaratan ƴan jarida irin su Jega da AbdulAziz su yi masa aiki da kwarewar su don ganin sun tallata shi a yankin Arewa kuma ya samu karbuwar da zai sa ya yi nasara a zabe mai zuwa.