NAFDAC ta yi gargadi game da illar shan maganin kara karfin maza mai suna ‘PrimeZen Black 6000mg’

Hukumar kula da ingancin abinci da magunguna ta kasa NAFDAC ta gargadi mutane da su nisanta kansu da yin amfani da maganin karfin maza mai suna ‘PrimeZen Black 6000mg’.

Maganin PrimeZen Black 6000mg magani ne da Kamfanin hada magunguna dake kasar Amurka ‘Volt Candy, 324 S. Diamond Bar Blvd #212’ yake hada wa.

Shugaban hukumar NAFDAC Mojisola Adeyeye ta yi wannan gargadi a farkon wannan mako yayin da ta yi karin bayani cewa Hukumar Kula da magunna na kasar Amurka ta gano cewa maganin na kunshe da sinadarin ‘Tadalafil da Sildenafil’ da ke iya cutar da lafiyar mutum.

Hukumar ta ce ana amfani da sinadarin Tadalafil da Sildenafil wajen kawar da matsalolin rashin jin shi’awar mace a jikin namiji sai dai kuma wadannan sinadarori na iya cutar da mutum idan har ya hadu da sinadarin ‘Nitrates’.

Shi Kuma sinadarin ‘Nitrates’ akan same shi ne a cikin magungunan da masu hawan jini da cututtukan dake kama zuciya ke amfani da su.

Hukumar ta yi wannan gargadi ganin cewa mutanen da suke fama da cututtukan zuciya da hawan jini ne za su fi amfani da wannan magani inda yin hakan ka iya kawo shanyewar bangaren jiki, hypotension da dai sauran su.

NAFDAC ta yi kira ga mutane da su guji amfani da magani tare da Kai karan duk wanda ke siyar da magani.

Hukumar ta yi kira ga mutane da su yi gaggawar zuwa asibiti a duk lokacin da aka samu matsala dalilin amfani da maganin.