A DAINA CIN GANDA: Gwamnati ta gargaɗi mutane su daina cin ganda don guje wa kamuwa da cutar ‘Anthrax’

Gwamnatin Najeriya ta gargadi mutane su daina cin naman daji da ganda domin guje wa kamuwa da cutar Anthrax.

Ma’aikatar inganta aiyukkan noma da yankin karkara ta gwamnatin tarayya FMARD ta sanar da haka.

A wata sanarwa dake dauke da sa hannun babban sakataren ma’aikatar Ernest Umakhihe gwamnati ta ce cutar Anthrax ya fara yaduwa a kasashen dake Kudu da Saharan Afrika da suka hada da Arewacin Ghana, Burkina Faso da Togo.

Menene cutar Anthrax

Cutar Anthrax cuta dake kama dabbobin gida da na daji.

Mutum na iya kamuwa da cutar idan yana yawan kusantar dabban dake dauke da cutar ko kuma idan ya ci naman daban da ya kamu da cutar.

Sai dai kuma cutar bata yaduwa a tsakanin mutane sai dai daga jikin daba zuwa mutum.

Alamun cutar sun hada mura, zazzabi, tari, ciwon jiki sannan idan har ba a yi gaggawar shan magani ba cutar na iya rikida zuwa cutar sanyi dake kama hakarkari da mutuwa.

Hanyoyin guje wa kamuwa da cutar

Likitocin dabobbi sun bayyana cewa yi wa dabbobi allurar rigakafin cutar na daga cikin hanyoyin dakile yaduwar cutar.

Za a iya samun maganin yin allurar rigakafin a babban asibitin dabbobi na kasa dake Vom jihar Filato.

Likitocin sun ce a ruka killa r dabbobin da suka kamu da wannan cuta domin gudun yadawa a tsakanin wasu dabbobin.

Sun kuma ce dabbobin da basu kamu da cutar ba ne kawai za a iya yi wa allurar rigakafin cutar.