Gwamnan Zamfara ya yi alkawarin kawo karshen rashin tsaro a jihar

Gwamna Dauda Lawal na jihar Zamfara ya yi alkawarin kawo karshen hare-haren ‘yan bindiga a jihar.
A wata sanarwa da kakakin gwamnan Suleiman Bala ya fitar gwamna Lawal ya fadi haka ne a jawabin da yayi lokacin da ya kai ziyara jaje karamar hukumar Tsafe wajen yin ta’aziyar wadanda yan bindiga suka kashe a harin da suka kai yankin.
Daga nan Lawal ya ziyarci fadark sarkin Tsafe, Muhammadu Bawa inda ya shaida masa cewa ya yi zama da jami’an tsaro na jihar domin tattauna yadda za a samar da tsaro dawwamammiya a jihar.
Gwamna Lawal ya shaida wa sarkin cewa ya yi zama da shugaban kasa Bola Tinubu kuma ya tabbatar masa cewa zai taimaka wa jihar wajen samar da tsaro a jihar.
Sannan kuma ya tattauna da gwamnonin yankin Arewa maso Yamma domin tsara hanyoyin da za a bi domin kawo karshe rashin tsaro a yankin.