A Cikin Kasashe 12, Ciki Har Da Najeriya, Aka Samu Bulluwar Nau’in COVID-19 Na Omicron

Najeriya ta shiga jerin kasashe 12 a fadin duniya da aka samu bulluwar sabon nau’in cutar coronavirus da ake kira Omicron. Nau’in cutar da aka gano a kudancin nahiyar Afrika ya shigo Najeriya ne ta hanyar wasu matafiya biyu da suka zo kasar daga Afrika ta kudu.