KATSINA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Har yau alƙalin Katsina na hannun masu garkuwa, kwanaki 27 bayan kama shi

Kwanaki 27 bayan da masu garkuwa su ka kama Mai Shari’a Shehu Yakubu shi da ƙanuwar matar sa, har yau su na hannun su ba su sake su ba.

‘Yan bindiga sun kama Shehu Yakubu tsakanin Funtua da Sabuwa, a kan hanyar sa ta komawa Funtua, lokacin da ya ke barin Sabuwa, garin da ya ke Alƙalin Kotun Shari’a.

An kama Shehu Yakubu tare da ƙaruwar matar sa a cikin daji, sannan kuma aka banka wa motar sa ƙirar Fijo 406 wuta.

Ƙanin sa mai suna Mustapha Yakubu, ya shaida wa wakilin mu cewa tun da aka kama alƙalin sau biyu kawai ‘yan bindiga su ka kira, su ka nemi a biya kuɗin fansa.

“Sun kira sun nemi a biya su naira miliyan 15. Mu ka ce ba mu da wannan kuɗin. Daga nan an riƙa ja-in-ja kan abin da su ka nemi a biya su.

“Ka san babu ‘netwok’, ba a iya kiran wayoyi. Daga nan ba mu ƙara jin su ba. Ba mu san halin da ake ciki ba.”

Mustapha ya yi kira ga hukuma da gwamnati a taimaka a kuɓutar da yayan na su.

Premium Times Hausa ta buga labari a ranar Laraba cewa mahara sun sake yin garkuwa da wani basarake a Katsina.

Wasu gungun ‘yan bindiga sun dira garin Fankama, inda su ka yi gaba da Dagacin gari mai suna Ahmed Sa’idu da matar sa da kuma wasu mutane da dama.

Garin Fankama na cikin Ƙaramar Hukumar Faskari a jihar Katsina. Faskari ta yi iyaka da ƙaramar hukumar Tsafe ta Jihar Zamfara.

Rahotanni daga yankin sun ce ‘yan bindigar ba su kashe kowa ba, amma sun shafe aƙalla sa’o’i biyu a cikin garin.

Wani ɗan uwan basaraken da aka yi garkuwa da shi mai suna Bahisullah Alhassn, ya shaida wa wakilin mu cewa an kwashe sauran iyalan basaraken waɗanda su ka raje a garin Fankama.

Ƙaramar Hukumar Faskari na ɗaya daga cikin ƙananan hukumomin da ‘yan bindiga ke addaba babu ƙaƙƙautawa.

Sace Dagacin Fankama ya da matar sa ya faru makonni biyu bayan mahara sun sako Dagacin Banye, basaraken da su ka kama bayan ya shafe kwanaki 26 a hannun su.

‘Yan bindiga sun sako Dagacin Banye, Bishir Giɗe, wanda suka kama kwanaki 26 da suka gabata.

Garin Banye ya na cikin Ƙaramar Hukumar Charanci ta Jihar Kstsina.

‘Yan bindigar sun kuma sako wani yaro ɗan sakandare da suka kama tare da Bishir Giɗe.

Wani ɗan uwan dagacin da mai suna nura, ya tabbatar da kuɓutar basaraken, bayan ya ji ta bakin makusantan Bishir Giɗe daga Banye.

Sai dai kuma bai san ko nawa aka biya ba kafin a sako shi tare da ɗalibin a ranar Laraba da yamma.