Da Ɗumi-Ɗumi: An sassauta tsauraran matakai da aka ɗaukan kan cin kasuwanni a Zamfara

Gwamna Bello Mohammed Matawalle ya sanar da sake buɗe wasu zababbun kasuwanni a jihar na ɗan wani lokaci domin sauƙaƙa wa al’ummar daga halun matsi da tsauraran matakan da gwamnatin jihar ta dauka a baya ya jefasu a ciki.

Kasuwannin da aka buɗe sun haɗa da Kasuwan Dabbobi a Gummi, Bagega, Danjibga, Kasuwar Daji, Tsafe, Talata-Mafara da kuma Nasarawar Godel.

  • Da Ɗumi-Ɗumi: An sassauta tsauraran matakai da aka ɗaukan kan cin kasuwanni a Zamfara
  • “A gaban ido na ƙanina Sani ya rasu babu abin na iya yi”- Ɗangote

Gwamna Matawalle ya bayyana hakan ne a ranar Juma’a yayin rantsar da kwamishinoni guda biyu da masu ba da shawara na musamman guda 10 da sakatarorin dindindin 8 da kuma sabon babban mai binciken kudi na gwamnatin jihar, kamar yadda yake ɗauke cikin jawabin manema labarai da Kakakin Gwamnan Zailani Bappa ya fitar.

Gwamna Matawalle ya ce matakin sake buɗe waɗannan kasuwannin ya biyo bayan ci gaba da aka samu a fannin tsaro a jihar a cikin wata ɗaya da kuma nuna damuwar gwamnatin kan halin ƙunci da rufe kasuwannin ya janyo ga tattalin arziƙin ƙananan hukumomi.

Sai dai Gwamna Matawalle ya yi gargaɗin cewa gwamnati, daga yanzu ba za ta ƙara lamuntar duk wani mutum ko ƙungiyoyi da ke kashe mutane ba da gangan a kasuwanni kamar yadda aka samu a baya.

“Duk wanda aka kama yana karya wannan doka zai fuskanci fushin doka da ya dace. Don haka ina kira ga kungiyoyin ‘yan banga da wadanda abin ya shafa da su bi doka da oda wajen magance duk wata matsala da ka iya tasowa a irin wannan yanayi.” Inji Gwamna Matawalle.

Gwamna Matawalle ya ci gaba da yin ƙira ga sarakunan gargajiya da sauran shugabannin al’umma da su tabbatar an sanya ido tare da daidaita wannan sabon matakin domin samun nasara ta yadda za a samu a sassauta tsauraran matakai a kan lokaci.

Gwamnan ya kuma yi ƙira ga jami’an da aka rantsar da su bayar da gudunmuwar su don ganin an samu zaman lafiya da kwanciyar hankali a jihar. Kamar yadda aka saba, an rantsar da jami’an ne tare da kur’ani mai tsarki domin tabbatar da basu da dangantaka da ƴan bindiga da ayyukansu a jihar.