Shin da gaske ne akwai wuraren kiwo a wasu kasashen duniya da suka fi fadin wasu jihohin Najeriya kamar yadda Gwamna Bagudu na Kebbi ya fadi? Binciken DUBAWA

Rikicin manoma da makiyaya a Najeriya na ci gaba da kasancewa karfen kafa ga masu ruwa da tsaki a lamarin a duk fadin Najeriyar. Rikice-rikicen wadanda suka yi sanadiyyar rayuka da dama wasu da yawa kuma suka rasa matsugunnensu sun sanya gwamnati nemo hanyoyin shawo kan matsalolin da yaki ci yaki cinyewa.

A wani rahoton Reliefweb wanda aka wallafa a shekarar 2018, riciki tsakanin makiyaya da manoma ya tsananta kuma ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 1,300 daga watan Janairun bana. Ana kyautata zaton cewa wannan adadi ya karu tunda a kullum kafafen yada labarai na ruwaito labaran kashe-kashe da ake yi sanadiyyar rikicin fulani da makiyaya.

A jihar Benue kadai ana kiyasin mutane sama da 2,000 suka mutu yayin da wasu akalla miliyan 1.5 kuma ke tsugunne a sansanonin ‘yan gudun hijra wato IDP camps a jihar, tun lokacin da rigingimun suka yi tsanani daga shekarar 2017 zuwa 2021.

A yunkurinsa na dakile wannan matsala, shugaba Muhammadu Buhari ya umurci wani kwamiti kwanan nan da ya yi bitan wasu wuraren kiwo da burtaloli 368 wadanda ke jihohi 25 a kasar domin tantance yawan wuraren da aka ratsa da gonaki ko gidaje, sai dai wannan mataki ya gamu da kakkausar suka da adawa daga bangarori daban-daban na kasar.

Yayin da yake bayani dangane da wannan batu, gwamnan jihar Kebbi, Atiku Bagudu ya ce akwai kasashen da ke da wuraren kiwo da suka ma fi wasu daga cikin jihohin Najeriya girma.

Gwamnan ya yi wannan bayani ne a wata hira da aka yi da shi a gidan talbijin na Channels.

Bagudu wanda ya yi tsokaci kan yawaitan rikicin makiyaya da manoman a Najeriya ya ce gano wuraren kiwon da aka kebe a baya zai taimaka wajen rage yawan rikicin.

Gwamnan ya ce umurnin shugaban kasar bai hana batun killace shanun Fulani a rugage su yi kiwonsu ba.

An dai ambato shi ya na cewa “an baiwa kwamitin nauyin gano burtalin kiwo kuma zai yi aiki da jihohin wajen zana su. Wannan ba dan a maido burtalolin ba ne illa dan gano matsalolin da ke tattare da su.

Tantancewa

Dubawa ta fara da tantance fadin Najeriya baki daya. Bisa bayanan Bankin Duniya a shekarar 2018 Najeriya na da girman fadin kasa 910770sq. Km

Ofishin jakadancin Najeriya a Birtaniya ita kuma ta ce jimilar yankin ya kai 923,770 km2 jimilar kasa 910,770 da gabar ruwan da ke da fadin 853 km

Kasar ta kasu zuwa jihohi 36 hade da birnin tarayyar. Jihar Legas ce mafi karancin fadin kasa dake da fadi 3,671km², sai jihar Anambra a 4,865 km²; sai jihar Abia da 4,900 km²; sai jihar Imo da 5,288 km².

Sauran jihohin sun hada da: Ekiti: 5,435km²; Ebonyi: 6,400km²; Akwa Ibom: 6,900km² a yayin da suaran jihohi 12 na tarayyar sun kasance tsakanin 7, 534km² and 23, 561km².

Wannan rahoton ya samo wadannan alkaluma ne daga Hukumar Kula da Yanayi ta Najeriya.

Da Dubawa ta ci gaba da bincike ta gano cewa daya daga cikin rugagen Australia wanda ake kira mafi girma a duk fadin duniya, ita ce mai suna Anna Creek Station na da fadin 23,677 Km sq. a tsakiyar Australiyar.

Haka nan kuma akwai Clifton Hills wanda ake gani shi ne filin noma mafi girma dake da fadin 16,500 km sq.

Australia ce ta uku wajen fitar da naman shanu a duniya inda take fitar da tonne miliyan daya da rabi na nama kowace shekara a cewar sashen kula da ayyukan noma na Amurka.

A karshe
Hakika akwai rugagen da suka fi wasu jihohin Najeriya fadi kamar yadda Bagudu ya fada.