Jarirai 27,490 ne aka haifa a asibitocin Kano banda na gida wanda babu lissafin su a cikin wata uku

Gwamnatin jihar Kano ta bayyana cewa jarirai 27,490 ne aka haifa a asibitocin dake fadin jihar cikin watanni uku da suka gabata.

Shugaban hukumar kula da asibitocin jihar Nasiru Alhasan ya sanar da haka a taron raba kayan aiki ga asibitocin jihar.

Alhasan wanda shugaban fannin kiwon lafiya na hukumar Sulaiman Hamza ya wakilta a taron ya ce an haifi jarirai 681 ta hanyar fida daga cikin jarirai 27,490 din da aka haifa a asibitocin jihar.

Sai dai ya ce adadin yawan jariran da aka haifa a jihar a wannan lokaci sun dara jarirai 27,490 din da aka haifa a asibitoci domin jihar na daga cikin jihohin dake da yawan mata da basu haihuwa a asibiti.

Alhasan ya ce haihuwa kashi 21.5% daga cikin haihuwa 10 ne kadai kwararriyar ungozoma ke karba a jihar.

An gano haka ne daga sakamakon binciken da ‘Nigeria Health Watch’ ta gudanar a shekarar 2020 a asibitoci 49 dake kananan hukumomi 44 dake Kano.

Binciken ya nuna cewa asibitocin da suka kware a lafiya mata da yara kanana basu da yawa a jihar.

Alhasan ya jinjina goyan bayan da suka samu daga kungiyoyin da suka hada kawance da su sannan ya yi kira ga attajirai, kungiyoyin kare hakkin dan Adam, kungiyoyin dake zaman kansu da su mara wa gwamnati baya don ganin an inganta fannin kiwon lafiya a Kano.

Jihar Kano na daga cikin jihohin kasar nan dake fama da yawan mace-macen mata da yara kanana.

Bincike ya nuna cewa mata 1,025 ne ke mutuwa wajen haihuwa daga cikin mata 100,000 duk shekara a jihar.