Najeriya ta tsaurara tsaron kurkukun Katsina, Kebbi da Gusau, don hana farmakin ‘yan ta’adda

An tsaurara matakan tsaro a gidajen kurkukun Katsina, Kebbi da Gusau domin hana ‘yan ta’adda kai harin kuɓutar da ‘yan uwan su da ke ɗaure a ciki.
Hakan ya faru kwanaki 11 bayan PREMIUM TIMES ta buga labarin da rahoton Hukumar Leƙen Asiri ta Sojoji, mai nuni da cewa ana shirin kai wa gidajen kurkukun hari.
A Katsina, Kakakin Yaɗa Labaran Hukumar Gidajen Kurkuku, Najib Idris, ya ce an tsaurara tsaro ne saboda hana kai harin.
Wakilin mu ya lura an tsaurara tsaro a Kurkukun Unguwar Yari da sabon kurkukun hanyar Jibiya.
Kamar yadda aka tsaurara tsaron a Katsina da sauran hanyoyin shiga cikin garin Katsina, haka aka tsaurara tsaron a kurkukun Gausu da wasu wurare da kuma na Kebbi.
Abin Da Ya Sa Aka Tsaurara Matakan Tsaro Gidajen Kurkukun Katsina, Gusau Da Kebbi:
Kwanan baya PREMIUM TIMES ta buga labarin da Hukumar Leƙen Asiri ta Sojoji ta bada rahoton cewa ‘yan ta’adda na gagarimin shirin kai hare-hare a garuruwa uku.
Wata majiya a cikin Hukumar Leƙen Asiri ta Sojoji ta ce ‘yan ta’adda na shirya gagarimin kai hare-hare a Gusau, Birnin Kebbi da Katsina don su fasa gidajen kurkuku su fitar da ‘yan uwan su da ke kulle a garuruwan uku.
Tuni dai har an aika da wannan gargaɗi ga Hukumar Kula da Gidajen Kurkuku ta Ƙasa (NCS).
Sun tsara fara kai harin a garin Gusau, daga nan kuma sai a Birnin Kebbi, sai kuma kurkukun na uku da za su fasa shi ne na Katsina. Haka dai hukumar ta leƙen asiri ta sanar da hukumar gidajen kurkuku, kamar yadda wani jami’in da ya san komai kan wasiƙar gargaɗin wadda ‘yan leƙen asiri su ka aika ga hukumar kurkuku, shi kuma ya shaida wa PREMIUM TIMES. Wannan jarida ta ga kwafen takardar gargaɗin da idon ta.
Majiyar ta ce matakin harin da ‘yan ta’adda za su kai daki-daki shi ne saboda ba su da isassun hanyoyin sufuri ko zirga-zirgar kai hare-haren lokaci ɗaya a garuruwan uku.
Dukkan garuruwan dai a yankin Arewa maso Yamma su ke, yankin da ke fama da ‘yan ta’adda da ‘yan bindiga su ke cin karen su babu babbaka. Haka nan kuma ƙungiyoyi irin su Boko Haram, Ansaru da ISWAP sun kwarara cikin yankin a ‘yan shekarun nan daga Arewa maso Gabas.
Haɗin kan da ya faru tsakanin Boko Haram da Ansaru ne ya haifar masu da samun nasarar harin da su ka kai a Kurkukun Abuja da ke Kuje, a ranar 6 Ga Yuli. Haka dai masu bincike da kuma manaƙalta hare-haren ta’addanci su ka bayyana.
A cikin wani bidiyo na baya-bayan nan da aka nuno maharan jirgin ƙasa na dukan waɗanda ke tsare sa hannun su, an ji wani ya na cewa ya na cikin waɗanda su ka kuɓuta daga Kurkukun Kuje.
Waɗannan mahara sun sha cewa gwamnatin tarayya ta san abin da su ke buƙata bai wuce a saki mutanen su da ke tsare ba.
Majiyar leƙen asiri ta ce buƙatar maharan ita ce a sako masu dukkan waɗanda ke tsare, su kuma za su saki fasinjojin da ke tsare a hannun su tun ranar 28 Ga Maris.
A cikin wannan gargaɗi na baya-bayan nan, gargaɗin leƙen asiri ya ƙarfafa cewa akwai yiwuwar su fara kai hari a kurkukun Gusau wannan Juma’a, 29 Ga Yuli.
Ranar Juma’a Kuma?:
Bayanan sirri sun nuna cewa za su iya kai harin ne a ranar Juma’a, saboda a ranar duk manyan jami’an kurkuku ba su wurin, ko dai sun rankaya hutun ƙarshen mako, ko kuma su na gida kwanciyar su.
To a lokacin ne ‘yan ta’addar za su bi ta wasu hanyoyin sirri su bai wa ƙananan jami’an kurkukun cin hanci domin a shigar wa ɗaurarrun da wayoyin kira.
Wani ƙwararren masanin tuggun yadda ‘yan bindiga ke tuntuɓar junan su, ya ce ta hanyar waya ne kaɗai maharan ke aikawa da saƙonni ko yin magana da ɗaurarrun da ke tsare a kurkuku.
Ya ce sai dai kuma wata dabara da ‘yan ta’addar ke yi, da sun gama waya sai su karairaya layin wayar.
Wani jami’in tsaro ya ce an samu layukan waya masu yawan a bayan kurkukun Kuje, bayan an gallaza wa wani da ake tsare da shi ya fallasa yadda ya yi magana da wasu na waje.
Yada Zangon Wucin Gadi A Unguwannin Kusa Da Kurkuku:
Rahoton sirri ya nuna cewa ‘yan ta’adda sun shirya yadda za a tura wasun su zaman wucin gadi a unguwannin da ke da kusanci da gidajen kurkuku, ya yadda za su riƙa kai makamai a unguwannin su na tarawa kafin su kai harin.
A Gusau, bayanin sirri ya nuna cewa za su fara yada zango ne su na sajewa da mutanen Unguwar Gwaza, kusa da kurkukun Gusau.
A kuma rahoton leƙen asiri na sojoji sun nuna a unguwar Ƙofar Soro maharan za su narke da sauran mutanen unguwa kafin su kai hari a Kurkukun Katsina. Sun kuma shirya kai harin cikin watan Agusta.
Sun shirya tura wasu mahara sajewa cikin mutanen unguwar da ake kira Kwaido cikin Ƙaramar Hukumar Augie.
Rahoton ya nuna mai yiwuwa ma tuni maharan sun shige cikin unguwannin na kusa da gidajen kurkukun.
Yayin da bayanan hukumar leƙen asiri ta yi kira a ƙarfafa tsaro a gidajen kurkuku, shi kuma Kakakin Gidajen Kurkuku na Ƙasa, Abubakar Umar, ya ce ba zai ce komai a kan bayanan sirrin ba.
Amma dai ya ce an ƙarfafa matakan tsaro a gidajen kurkuku, tun bayan farmakin da ‘yan ta’adda su ka kai a Kurkukun Kuje.