MAKON SHAYARWA: An samu karin kashi 27% na yawan matan dake shayar da ‘ya’yan su ruwan momo zalla a jihar Anambra

Hukumar kula da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko ta jihar Anambra (ASPHCDA) ta bayyana cewa jihar ta samu karuwa a yawan matan dake shayar da ‘ya’yan su nono zalla daga Kashi 17% a shekaran 2018 zuwa Kashi 27% a 2022.

Shugaban hukumar na jihar Chioma Ezenyimulu ta sanar da haka a taron makon shayarwa ta shekaran 2022 da aka yi a Amawbia dake Awka ranar Alhamis.

An kebe ranar 1 zuwa 7 ga watan Agusta ta kowace shekara domin wayar da kan mutanen mahimmancin mata su shayar da jariran su nono zalla domin inganta lafiyar su.

Taken taron bana shine: Zage damtse domin wayar da kan mutane

Ezenyimulu ta ce jihar ta samu wannan karuwa ne a dalilin wayar da kan mutane da aka rika yi a asibitoci da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko.

“Muna murna da samun karin kashi 27% din da aka yi amma har yanzu akwai sauran aiki da ya kamata a yi domin cin ma burin samun kashi 50% daga nan zuwa shekaran 2025 a jihar.

“Muna kira ga mutane da su mara mama baya wajen ganin an ci gaba da wayar da kan mutane mahimmancin shayar da yara nono zalla.

“Shayar da jariri nono zalla dabara ce dake taimakawa wajen inganta lafiya da da mahaifiyarsa.

Kwamishinan lafiya na jihar Afam Obidike ya ce wannan gwamnati ta hada karfi da karfe domin ganin ta inganta lafiya mata da yara kanana a jihar.

Obidike ya yi kira ga mazaje da su rika karfafa gwiwowin matansu wajen ganin sun shayar da ‘ya’yan su nono zalla domin kare ‘ya’yan su daga kamuwa da matsalar yunwa da cututtukan dake kaisan yara kanana.