SOYAYYAR FACEBOOK: Muhibbat ta roki kotu ta raba aurenta da mijinta da suka haɗu ta Facebook saboda zargi

Kotun Majistare ta Grade A dake Mapo a Ibadan jihar Oyo ta raba auren shekara 8 tsakanin Muhibbat Lawal da mijinta Abduljelil Lawal a dalilin rashin soyayya a tsakanin su.
Muhibbat ta ce ta hadu da mijinta Lawal a Facebook daga nan suka fara soyayya har suka yi aure a garin Offa kuma sun haifi ‘ya’ya biyu.
Ta ce bayan sun yi aure ne Lawal ya canja mata ya fara cin mutuncinta da cin zarafi ta.
“Lawal kan lakada min duka a duk lokacin da na tambaye sa kudi sannan a kulum yana zargina wai ina yawan neman maza a waje.
Muhibbat ta roki kotun ta raba auren saboda babu sauran soyayya a tsakanin ma’auratan.
Shi ko Lawal ya musanta duk laifin da Mug’hibbat ta ce ya aika kuma ya amince kotu ta raba auren, shima ya gaji.
Lawal ya ce shima ya gaji da auren kuma yana rokon kotu ta bashi damar kula da ‘ya’yan.
Alkalin kotun S.M. Akintayo ta raba auren sannan ta bai wa Muibat ikon kula da ƴaƴan natsu. Ta kuma umarci Lawal ya rika ba Muhibbat naira 15,000 duk wata don ciyar da su da kula da su.
Amma kotu ta ce maganar makaranta, su biyun ne za su rika kula da ƴaƴan suna biya musu kuɗin makaranta. Sannan kuma kowa ya kama gabansa daga yau.