2023: Dalilin soke ‘yan takarar PDP 2 daga cikin 17 da aka tantance – David Mark

Jam’iyyar PDP ta bada sanarwar soke ‘yan takarar shugaban ƙasa biyu daga cikin 17 ɗin da ta tantance.
Shugaban Kwamitin Tantance ‘Yan Takara na PDP, Sanata David Mark ne ya sanar da haka, jim kaɗan bayan kammala aikin tantancewar, a Hedikwatar Kamfen ɗin PDP ta Legacy House, Abuja, a ranar Juma’a.
Mark ya ce sun tantance ‘yan takara har 17, amma a ciki sun soke takarar mutum biyu, bisa dalilan rashin cancanta.
Ya ce sun shafe tsawon sa’o’i 10 cur su na aikin tantancewar.
Yayin da ya ke shaida wa manema labarai soke ‘yan takara biyu, Mark bai bayyana sunayen su ba.
“Mun tantance ‘yan takara 17, mutum 15 za su yi takarar zaɓen fidda gwani, amma mun soke takarar mutum biyu.
“Amma kada ku tambaye ni sunayen waɗanda aka soke takarar su da waɗanda ba a soke ta su takarar ba. Saboda ko kun tambaya ba za ni karanto maku sunayen su ba.”
Sai dai ya jaddada cewa an soke takarar mutum biyu ɗin saboda ba su cika sharuɗɗan shiga takarar ba, shi ya sa ba su cancanta ba.
Da aka tambaye shi sai yaushe kwamitin su zai damƙa wa uwar jam’iyya sunayen waɗanda aka tantance ɗin, sai Mark ya ce “yau ɗin nan da dare.” Wato ya na nufin jiya Juma’a kenan.
Mark ya ce waɗanda aka soke sunayen na su na da damar ɗaukaka ƙara ga Kwamitin Ɗaukaka Ƙara na PDP.
Ya ce kwamitin ya gamsu da cancanta da kuma nagartar waɗanda aka tantance ɗin, ya na mai cewa duk wanda ya yi nasara a zaɓen fidda gwani a cikin su, shi zai lashe zaɓen shugaban ƙasa.
Waɗanda aka tantance ɗin sun haɗa da Atiku Abubakar, Bukola Saraki, Pius Anyim, Peter Obi, Bala Mohammed da Aminu Tambuwal.
Akwai kuma Nyesom Wike, Dele Momudu, Hayatuddeen Mohammed, Sam Ohabunwa, Emmanual Udom da kuma mace ɗaya tilo, Olivia Tariela.
Sauran sun haɗa da Ayo Fayose, Charles Okwudili, Chikwendu Kalu da Cosmos Ndukwe.
PDP dai ta shirya yin zaɓen fidda-gwani a ranar 14 Ga Mayu, 2022.
Sai dai kuma har yau ba ta ce komai ba a kan batun yankin da ɗan takarar shugaban ƙasa zai fito da kuma tsarin zaɓen da za ta bi wajen fito da ɗan takarar ta.