BA A BORI DA SANYIN JIKI: Ken Nnamani ya fito takarar shugaban ƙasa a APC, ya karaya da farashin fam ɗin naira miliyan 100

Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Ken Nnamani ya fito takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar APC.
yayin da ya ke bayyana fitowa takarar sa a ranar Juma’a, Nnamani ya koka a kan tsadar kuɗin fam ɗin rajistar takarar APC har naira miliyan 10.
Idan ba a manta ba, tun ranar da jam’iyyar APC ta tsaida Naira miliyan 100 kuɗin sayen fam ɗin takarar shugaban ƙasa ne jam’iyyar ke ci gaba da shan suka da caccaka.
Yayin da ɗan takarar gwamna zai lale naira miliyan 50 kuɗin fam, mai takarar sanata zai biya naira miliyan 50, shi kuma ɗan majalisar tarayya naira miliyan 10.
Shi dai Ken Nnamani ya ce tsadar farashin takarar shugaban ƙasa bai yi lebur da haƙiƙanin halin ƙarfin aljihun ɗan Najeriya ba.”
Ya ce duk da dai ƙarfin wani ba ɗaya da wani ba, to yanzu a Najeriya iyar ƙarfin samun da ke shiga aljihun ka, iyar matsalolin da ke kan ka da hidimomin yau da kullum.
Ya ce akwai buƙatar a sake duba tsadar farashin fam ɗin takarar APC ba don komai ba, ko don a sake sabon lale, ta yadda za’a bayar da dama matasa da mata da sauran ‘yan Najeriya masu ƙaramin ƙarfi za su iya shiga a dama da su.
Haka kuma Nnamani ya ce akwai buƙatar Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fito da tsari da kuma ƙa’idar adadin kuɗin kowane muƙami da za’a yi takara a lokacin zaɓe.
“Wataƙila akwai buƙatar INEC ta fito da ƙa’idoji da sharuɗɗan adadin farashin fam ɗin takara da kuma adadin kuɗaɗen da kowace jam’iyya ko ɗan takara zai kashe a lokacin zaɓe.
Sai dai kuma duk da kiraye-kirayen ake yi na tsadar kuɗin sayen fam ɗin takara, APC ta yi kunnen-uwar-shegu, ta ƙi rage kuɗin.
Maimakon ta rage, APC na ci gaba da kare farashin, inda a farkon wannan mako Shugaban APC Abullahi Adamu ya bayyana cewa kuɗin ba su yi tsada ba.
“Idan ɗan takara ba shi da naira miliyan 100, babu abin da zai sa ya fito neman kujerar shugaban ƙasa.”
Nnamani ɗan asalin jihar Enugu, ya ce idan har dai za a yi wa yankin Kudu maso Gabas adalci, to shi ne ya fi dacewa ya tsaya wa APC takarar shugaban ƙasa.