2019 ZUWA 2021: An haifi jarirai sama da 17,000 a sansanin ƴan gudun hijira 18 a Barno

Ƙungiyar Masu Lura da Lamurran ‘Yan Gudun Hijira ta Ƙasa-da-ƙasa (IOM), ta bayyana cewa ƙididdiga ta tabbatar da an haifi jarirai 17,053 a sansanin ‘yan gudun hijira 18 cikin shekaru biyu da rabi a Jihar Barno.

Hukumar wadda ke ƙarƙashin Majalisar Ɗinkin Duniya, ta shaida cewa ta yi amfani da alƙaluman rajistar haihuwar ƙananan yara a sansanonin waɗanda aka yi wa rajistar haihuwa a tsakanin 2019 har zuwa watan Mayu, 2021.

Jagoran Jami’an IOM, Frantz Celestine, ya ce hukumar sa aiki tare da Hukumar Ƙidaya ta Ƙasa da kuma UNICEF ta na bayar da katin shaidar haihuwa ga duk wani jaririn da aka haifa a sansanin masu gudun hijira.

Ya ce ƙididdige yaran na da matuƙar muhimmanci, sannan kuma dama aikin ƙungiyar sa ne tattara bayanan jama’ar da aka raba da muhallan su, su ke zaune a sansanin masu gudun hijira.

Ya ce waɗannan bayanan ƙididdiga ana miƙa su ga cibiyoyin da ke bayar da agaji da tallafi ko shiga tsakani a Arewa maso Gabas.

“Mu na yin ƙididdiga ta domin mu san yawan mutanen da aka raba da gidajen su, ta yadda ayyukan agaji da jinƙai ɗin da ake yi masu zai yi masu tasiri sosai.

“Ƙididdigar nan ta na amfani wajen raba abinci ko wasu kayayyakin da ba abinci ba. Kuma ta na da amfani wajen raba magunguna.

“Yawan jariran da aka haifa kamar yadda na ga adadin bayanan, sun nuna tsakanin 2019 zuwa Mayu, 2021 an haifi jarirai 17,053.” Inji shi.

Ya ce ƙididdiga na sa a gane kuma a tantance waɗanda aka kora daga gidajen su, su ke gudun hijira.

“Domin idan ba a san da kai ba har aka tantance ka, to a ƙa’idar gwamnati da ƙa’idar doka, ba a san ka na raye a duniya ba.

“Amma abin takaici jama’a ba su san mu na wannan gagarimin aiki ba. Abin da kawai su ka san mu na yi, shi ne maida ‘yan gudun hijira gidajen su a Najeriya.”

Ya ce IOM ta cika shekaru 20 da kafawa.