ƁARKEWAR CUTAR SANYIN ‘DlPHTHERlA’: Kowa ya yi ta kan sa’, inji Gwamnatin Tarayya

Gwamnatin Tarayya ta yi gargadi kan cewa baba da yaro kowa ya yi ta kan sa, kada ya bari cutar Diphtheria ta kama shi.

Sashen Wayarwa da Gargadi na Ɓangaren Lafiya ya yi wannan gargaɗi a ranar Litinin, ya ce kowa ya yi nesa daga kamuwa da cutar.

Sashen ya ce cuta ce da ke kisa ba tantama, wacce ƙwayoyin halittar cuta ce ke haddasa ta.

Cutar na ɗarsashi a cikin jiki daga kwana biyu zuwa biyar, amma idan ta yi tsawo za ta yi har kwana goma.

“Ya zama wajibi musamman yara kasa da shekaru biyar da dattawa sama da shekaru 60 a kiyaye sosai.”

“Da ma yara waɗanda ba a gama yi masu allurar rigakafi ba, har jama’a su guji cinkoso da ma’amala da ƙazanta.

“Masu yawan fama da rashin lafiya su yi hattara. Masu tafiya a inda cutar ta shiga, a yi hattara. Haka a wurare da ba masu lura da harkokin lafiya.”

Wannan jarida ta buga labarin cewa cutar Sanyi ‘Diphtheria’, ta yi ajalin mutum 80 a Najeriya, cewar NCDC.

A farkon wannan wata, Kano ce a gaba, mutum 123 sun rasu, 38 na kwance a asibiti.

Hukumar Dakile Yaduwar Cututtuka ta Kasa NCDC ta bayyana cewa, cutar Diphtheria ta barke a Babban Birnin Tarayya Abuja inda mutum ɗaya ya kamu sannan ta yi ajalin mutum ɗaya ɗan shekara huɗu a watan Yuni.

Bisa ga wata takarda da hukumar ta fitar ranar Alhamis ya nuna cewa mutum 798 sun kamu da cutar a ƙananan hukumomi 33 da ke jihohi takwas da Abuja a watan Disambar 2022.

Zuwa yanzu cutar ta yi ajalin mutum 80 a Najeriya.

Diphtheria ta fi kama yara ƙanana a Najeriya.

NCDC ta bayyana cewa cutar ta fi yadtuwa a jihohin Kano, Lagos, Yobe, Katsina, Cross River, Kaduna da Osun.

Hukumar ta ce kashi 71.7% daga cikin mutum 798 din da suka kamu da cutar yara ne ƴan shekara 2 zuwa 14.

NCDC ta yi kira ga iyaye da su kai ‘ya’yan su ana yi musu allurar rigakafi domin samar musu kariya.

Cutar Diphtheria:

Cutar Diphtheria cuta ce da ƙwayoyin cutar bacteria mai suna ‘Corynebacterium’ke haddasa ta.

Cutar ta fi saurin kama yara da manya, musamman waɗanda ba su yi allurar rigakafin cututtuka da ake yi wa yara ba.

Cutar kan kama maƙogaro, hanci sannan wasu lokuta har za a farga mutum na yakunewa.

Cutar ya fi yaɗuwa idan ana yawan zama kusa da waɗanda suke ɗauke da ita, idan mai ɗauke da cutar ya riƙa yin tari ko atishawa a tsakanin mutane.

Alamun cutar sun haɗa da zazzabi, yoyon hanci, ciwon makogoro, idanu su yi jajawur, tari da kumburin wuya.

Wasu lokuta mai fama da cutar zai riƙa ganin wasu farin abubuwa na fitowa a kusa da maƙogaron sa wanda ke hana mutum iya yin numfashi.

Hanyoyin Samun Kariya Daga Cutar:

1. Yin allurar rigakafi.

2. Saka takunkumin fuska, musamman idan za a shiga cikin mutane.

3. Toshe baki da hanci idan za a yi tari ko atishawa.

4. Tsaftace muhalli, wanke hannu da ruwa da sabulu a kowani lokaci.

5. Zuwa asibiti idan aka kamu da zazzaɓi, ko idan ba a gane lafiyar jiki ba.