GABAS DA YAMMA KUDU DA AREWA: Mutum 123 kaɗai su ka fi Ɗangote kuɗi a duniya – Mujallar Forbes

Mashahuriyar mujalla mai bin diddigin ƙwalailaice adadin yawan kuɗaɗen da attajirai su ka mallaka a duniya, wato Forbes, ta bayyana cewa a 2023 Ɗangote ne lamba na 124 a jerin sunayen attajirai 200 a duniya.
Lissafin ya tabbatar da cewa tsawon shekaru 12 a jere Ɗangote ya tsare matsayin sa na 1 a Afrika.
Sai dai kuma shekarar 2023 ba ta zo wa wasu attajirai 254 a faɗin duniya da daɗi ba, domin kuwa gargada da tattalin arziki da shiga a duniya cikin 2022, ta watsar da su daga cikin jerin wadanda suka mallaki fiye da dala biliyan 1 a duniya. A yanzu a cikin su ba mai Dalar Amurka Miliyan 1.
Shi kuwa Ɗangote na sa Arziki ƙaruwa ya yi, daga dala biliyan 12.1 a 2022 zuwa dala biliyan 14.2 a 2023.
Ana sa ran Ɗangote za shi ƙara ɗagawa sosai a shekara mai zuwa, da zartar Matatar Ɗangote ta fara aiki.