Ƴan sanda sun kama mutumin da ya saba Yi wa mata fashi bayan ya zuba musu maganin barci a lemu

Rundunar ‘yan sandan jihar Legas ta kama Ifeanyi Ezennaya mai shekaru 36 da laifin sace wa mata shida wayoyin hannu su a jihar.
A lissafe dai jimlar kudin wayoyi shida na Iphone wanda ya sace musu ya kai naira miliyan hudu.
Rundunar ta ce Ezennaya ya yi wa wadannan mata fashi ranar Talatan da ta gabata a layin Falolu dake Surulere.
Sakamakon binciken da rundunar ta gudanar ya nuna Ezennaya ya lallabi wadannan mata zuwa wani daki a Otel ya zuba musu maganin barci a cikin lemu suka sha sannan bayan ya tabbatar kowacen su ta yi barci sai ya wawushe musu wayoyida wasu kayayyakin su masu daraja.
Daya daga cikin matan da Ezennaya ya yi wa fashi ta ce sun fara haduwa da Ezennaya yayin da suke bukin zagayowar ranar haihuwar daya daga cikin su a wani wurin shakatawa.
Ta ce a lokacin Ezennaya ya ce sunan sa Emeka kuma wai bai dade da ya dawo daga kasar Switzerland ba amma yana so ya zama abokin mu.
“Nan da man mutum biyu daga cikin mu suka bashi lambobinsu sannan suka karbi nashi.
“Bayan kwana biyu sai ya kira mu cewa yana so mu zo mu shakata tare da shi.
“Da muka je sai ya shigar da mu wani daki da ya karba a wani Otel sannan ya kawo mana lemu da wasu ababen sha.
Daga nan sai wata daga cikinsu ta ce tun bayan da suka kwankwaɗi lemun da Emeka ya basu suka bingire sai barci. Ba su farka ba sai da suka share awa 6 suna sharara barci.
Ta ce sun tashi sun ga Ezennaya ya sace wayoyinsu, agogunan hannu da sarkokin su na zinare da dai sauran su.
” Mun gano cewa Ezennaya ya siyar da wayoyin mu a Onitsha akan Naira 900,000 sannan ya cire naira 50,000 daga asusun bankin daya daga cikin mu.
Bayan haka ‘yan sandan dake Surulere sun kama Ezennaya a wani otel dake Allen Avenue dake Ikeja ranar Alhamis din da ta gabata dadai zai yi wa wata mata fashi.
Kakakin rundunar Benjamin Hundeyin ya ce Ezennaya ya saba zambatar mata ya yi musu fashi.