MONKEYPOX: Cutar ƙyandar biri ta kama Amurkawa 6,000

Makonni biyu bayan Hukumar Lafiya ta Majalisar Ɗinkin Duniya ta ayyana cutar ƙyandar biri matsayin sabuwar annobar da ta darkaki duniya, ƙasar Amurka ma ta ta bi bayan ta, har ta kafa wa cutar dokar ta ɓaci a faɗin ƙasar.

Ma’aikatar Lafiya da Inganta Rayuwar Jama’a ta Amurka (HHS) ce a ranar Juma’a ta bayyana cewa “daga cikin ƙoƙarin da Gwamnatin Biden da Haris ke yi, shi ne tabbatar da ganin cewa cutar ƙyandar biri wadda ta zama annobar, tilas za a ɗauki ƙwaƙƙwaran matakan daƙile ta da hana kamuwa da ita.”

Hukumar Daƙile Cututtuka Masu Yaɗuwa ta Amurka (CDC), ta ce fiye da mutane 6,000 ne su ka kamu da cutar a faɗin jihohi 48 da birnin Washington da kuma Puerto Rico ya zuwa ranar Alhamis.

Ya zuwa ranar Juma’a, CDC ta tabbatar da cewa waɗanda su ka kamu da cutar a duniya ciki ƙasashe 88, sun kai mutum 28,220.

CBC ta ce 81 daga cikin ƙasashen ba su ma taɓa samun wanda ya kamu da cutar ba, kafin wannan lokaci.

Wata sanarwa da HHS ta fitar kuwa cewa ta yi, “magance cutar ƙyandar biri babban abin da Gwamnatin Biden da Haris su ka sa a gaba ne, shi ya sa ma aka kafa wa cutar dokar ta-ɓaci.”

Sakataren Hukumar Lafiya Xavier Becerra ne ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar.

Sanarwar ta naƙalto Kodinetan Daƙile Cutar Ƙyandar Biri na Ƙasa da ke Fadar White House ya tabbatar cewa Amirka za ta yi amfani da darasin da ta koya daga korona, gobarar daji da wajen gaggauta kawar da ƙyandar biri a ƙasar.