Jami’ar Northwest Sokoto ta saka wa ginin ɗakunan ɗaliban ta sunan farfesa Adamu Gwarzo

Jami’ar Northwest dake Sokoto ta rangaɗawa ginin ɗakunan ɗalibai maza na jami’ar sunan Farfesa Adamu Gwarzo, shugaban jami’ar Maryam Abacha, da ke Kano.
Farfesa Gwarzo wanda sananne wajen bayar da gagarimar taimako da tallafi ga ilimi a faɗin nahiyar Afrika ya ziyarci wannan makaranta da kan sa yayin da yayi rangadi na musamman domin duba ginin wannan jami’a.
A wasika ta musamman wacce magatakardar jami’ar Umar Musa ya rattaba wa wannan ya ce jami’ar ta yi haka ne domin karrama Farfesa Gwarzo da kuma jinjina masa bisa tallafi da taimako da ya ke yi wa fannin ilimi a nahiyar Afirka.
A jawabin godiyar sa, Farfesa Gwarzo ya godewa jami’ar bisa wannan karamci da su yi masa,
Baya ga jami’ar Maryam Abacha dake Kano, farfesa Gwarzo ya kafa sabbin jami’o’i biyu, ɗaya a Kaduna, ɗaya a Abuja.