Mijina na taramin gajiya da yawan jima’i, na gaji da auren haka nan – Inji matar Sa’idu Lawal a Kotu

A ranar Juma’a ne Olamide Lawal ta shigar da kara a kotun gargajiya na Grade ‘A’ dake Mapo a Ibadan inda ta roki kotu ta warware aurenta na shekara 14 da mijinta Saheed Lawal.

Olamide ta kuma roki kotun ta hana Lawal kiranta a wayan salula da kawo mata ziyara gidanta.

A bayanin da ta yi Olamide ta ce mijinta mashayin giya ne sannan hariji ne wajen jima’i, yana lallasa ta matuka a kullum suka yi arangama wajen saduwa.

Ta ce a duk lokacin da Lawal ya sha giya sai ya lakaɗa mata dukan sannan ya tilasta ta dole su sadu ko tana so ko bata so.

“Duk da haka Lawal baya kula da ni ko ‘ya’yan da muka haifa tare.

Olamide ta ce ta gaji da auren mijin dake dukan ta, tilasta wajen yin jima’i sannan da rashin kula da iyalansa.

Lawal ya amince da duk abin da Olamide ta faɗi a a kotun sannan ya roki kotu ta taimaka wajen bai wa Olamide hakuri domin har yanzu yana son matar sa.

Lawal wanda tela ne ya yi alƙawarin cewa daga yanzu yayi sallama da kwankwaɗan giya kuma zai riƙa kula da iyalan sa matuƙa daga yanzu kuma zai daina lallasa ta da tsumagiya kamar yadda yake yi a baya.

Alkalin kotun S.M. Akintayo ya hori ma’auratan da su je su ci gaba da zaman lafiya a tsakanin su.

Akintayo ya ce za a ci gaba da shari’a ranar 1 ga Maris.